90% na masu cutar COVID-19 su na warkewa ne da kansu – Inji Darektan NCDC
Chikwe Ihekweazu, wanda shi ne babban Darekta Janar na hukumar NCDC mai takaita yaduwar cuta a Najeriya, ya yi magana game da yadda ake fama da annobar COVID-19.
Dr. Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa kashi 90 cikin 100 (90%) na duk wadanda su ka kamu da cutar ta Coronavirus, su na warkewa ba tare da an yi masu wani magani ba.
Ihekweazu ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya zanta da Manema labarai a Ranar Laraba, 8 ga Watan Afrilu, 2020. Jaridar The Cable ta kasar nan ta rahoto wannan a jiya.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, Chikwe Ihekweazu ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi masa tambaya game da yadda Seyi Makinde ya warke a cikin kasa da mako.
Idan ba ku manta ba kwanakin baya aka tabbatar da cewa kwayar cutar COVID-19 ta kama gwamnan jihar Oyo. Ba a dauki mako guda ba aka ji cewa gwamnan ya warke.
KU KARANTA: Coronavirus: Za a yi wa wadanda ke daure a gidan yari afuwa
Darekta Janar na hukumar NCDC ya yi wa jama’a karin haske da cewa abin da mai fama da cutar Coronavirus ya ke bukata shi ne a taimakawa jikinsa har ya warke da kansa.
“Mu tuna cewa 90% na Marasa lafiyan nan su na samun sauki ne ba tare da an yi masu komai ba, idan har ka sha wani abu, sai ka ce saboda shi ka warke, ba haka ba ne.”
Makinde ya yi ikirarin cewa karas da Bitamin C da zuma ya yi amfani da su a lokacin da ya ke jinya har ya samu sauki. Ihekweazu ya na ganin wadannan ba su da tasiri.
Shugaban hukumar ya ce mafi yawan kwayoyin cutan ‘Virus’ ba su da magani a Duniya. Ihekweazu ya ce ko na’urar numfashi da ake kafawa jama’a ba magani ba ce.
Kafin yanzu, karamin Ministan lafiya, Dr. Adeleke Mamora ya nuna cewa bai san yadda gwamna Seyi Makinde ya warke ba, Mamora ya fadawa ‘Yan jarida bai da masaniya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng