Gwamnatin Bauchi zata rage albashin ma'aikatan jihar don yakar Coronavirus

Gwamnatin Bauchi zata rage albashin ma'aikatan jihar don yakar Coronavirus

- Gwamnatin Bauchi ta rage albashin ma'aikatan jihar saboda Coronavirus

- Gwamnatin ta daurawa ma'aikatan yin sadakan da wani kaso albashin nasu domin yakar cutar a jihar

- Har yanzu gwamnan jihar, Bala Abdulkadir na kwance asibiti

A ranar Laraba, gwamnatin jihar Bauchi ta ce a watan Mayu da Yuni masu zuwa, ma'aikatan jihar ba zasu samu cikakken albashi ba, zasu sadaukar da wani kaso.

Babban mai magana da yawun gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki yau.

Ya ce kudin zai kasance gudunmuwar ma'aikatan ga gwamnati wajen yakar annobar Coronavirus.

Gidado ya ce an yi yarjejeniyar haka ne a zaman da shugaban ma'aikatan jihar, sakatarorin din-din-din, diraktoci da kungiyar kwadago suka yi ranar 3 ga Afrilu, 2020.

Yace a yarjejeniya, sakatarorin din-din-din da wadanda ke matsayinsu zasu bada kashi 10% na albashinsu na watannin Afrilu, Mayu da Yuni 2020.

DUBA NAN Dr. Ngozi Iweala ta jinjinawa yadda ake raba kayan abinci a kasar Ruwanda

Yace “Diraktoci masu daraja na 16 da 17 a jihar da kananan hukumomi zasu bada kashi 5% na albashinsu cikin watannin da aka ambata.“

“Maaikata daga matsayi na 1 zuwa 15 kuwa zasu bada gudunmuwar kashi 1% na albashinsu na watan Afrilu, Mayu da Yuni.“

Hadimin gwamnan ya ce shugaban Maaikatan jihar, Ahmed Ma’aji, da shugaban kungiyar kwadagon Najeriya, Danjuma Saleh, suka rattafa hannu kan takardar yarjejeniyar.

Sauran wadanda suka shaida sune shugaban TUC, Sabiu Barau, shugaban kwamitin yarjejeniyar, Dauda Shauibu.

A bangare guda, Gwamnatin tarayya ta aika sabon kasafin kudin tarayya majalisar dokokin tarayya domin sake dubawa saboda halin da kasa ke ciki na annobar cutar Coronavirus da fadin farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Kasafin kudin da Buhari ya tura kamar yadda wasu alkaluma suka bayyana ya ragu daga N10.594 trillion zuwa N10.276 trillion.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel