Kasar Dubai ta dakatar da aure da saki a lokacin annobar covid-19

Kasar Dubai ta dakatar da aure da saki a lokacin annobar covid-19

A wani hoto da aka dauka a ranar 28 ga watan Maris din 2020, an ga titin Dubai tamkar an share sakamakon barkewar annobar coronavirus.

Akwai yuwuwar annobar coronavirus din ta lalata zamantakewa. Amma a Dubai an dakatar da aure da saki har sai yadda hali yayi don gujewa taron da zai iya zama sanadin yaduwar cutar coronavirus.

Sashen shari'a na Dubai ya sanar da wannan hukuncin a ranar Laraba don samar da mafita wajen yaduwar muguwar annobar. Hakan kuwa na iya bada gudumawa wajen assasa dokar hana walwala a kasar.

Jastis Khaled al-Hawsni na kotun iyali ya kara da cewa, sashin shari'ar ya bayyana cewa jama'a masu tarin yawa a kasar sun cike sharuddan aure ta yanar gizo.

Don haka ba za a hana su gudanar da daurin aure ba, amma kada su hada liyafa "koda kuwa a cikin gida ne."

Kasar UAE na da mutane 2,000 da suka kamu da muguwar cutar covid-19, kuma mutane 12 ne suka rasa rayukansu, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya bayyana.

Kasar Dubai ta dakatar da aure da saki a lokacin annobar covid-19
Abu Dhabi, babban birnin kasar Dubai
Asali: UGC

Dukkan 'yan kasar da kuma mazauna kasar wadanda ba ayyuka na musamman suke yi ba, dole ne sai sun nemi izini kafin fita daga gidajensu.

DUBA WANNAN: Covid-19: Likitocin kasar China sun iso Najeriya (Bidiyo)

Dubai na daya daga cikin masarautu 7 da suka hada kasar UAE din. A halin yanzu dai dukkan ziyara ga manyan kantuna da otal na masarautar an dakatar.

Rayuwa a cikin dokar hana walwala ta jawo tambayoyi kala-kala daga 'yan kasar.

Wani mutum mazaunin daular larabawan ya tuntubi 'yan sanda a kan ko sai sun bashi izinin ziyartar matar shi ta biyu, jaridar Gulf News Daily ta ruwaito ba tare da bayyana amsar da ya samu ba.

A kasar dai an halasta auren mace fiye da daya kamar yadda dokar addinin Musulunci ta tanadar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel