Covid-19: Likitocin kasar China sun iso Najeriya (Bidiyo)

Covid-19: Likitocin kasar China sun iso Najeriya (Bidiyo)

Tawagar wasu kwararrun likitoci daga kasar China sun iso Najeriya duk da dawar da kungiyar likitoci da wasu mambobin majalisa suka nuna a kan kudirin gwamnatin tarayya na gayyato likitocin domin taimakawa a yaki da annobar cutar covud-19.

A wani takaitaccen sako mai hade da faifan bidiyo da gidan talabijin na TVC ya wallafa a shafinsa na tuwita, an ga isowar likitocin na kasar China suna magana tare da ministan lafiya a wani wuri da ya yi kama da filin saukar jiragen sama.

Kungiyar NMA ta Likitocin Najeriya da kuma TUC ta ‘Yan kasuwa sun nuna rashin amincewar su da gayyatar da gwamnatin tarayya ta yi wa Likitoci da Ungonzoma daga kasar Sin.

Wadannan kungiyoyi sun nuna cewa sam ba su tare da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wannan mataki da ta dauka na yaki da cutar Coronavirus da ta addabi kasashe.

A Ranar Juma’ar makon jiya ne ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya shaidawa Najeriya cewa wasu Malaman kiwon lafiya daga kasar Sin za so Najeriya domin taimakawa asibitocinmu.

Bayan haka, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa za a aikowa Najeriya kayan aikin asibiti wanda daga cikin har da na’urar taimakawa numfashi, wannan duk don a yaki cutar COVID-19.

Covid-19: Likitocin kasar China sun iso Najeriya (Bidiyo)
Ministan lafiya
Asali: Facebook

Sai dai shugaban kungiyar Likitoci a Najeriya, Dr. Francis Faduyile, a wani jawabi da ya fitar wanda ya shiga hannun Daily Trust, ya nemi gwamnati ta dakatar da wannan magana.

Francis Faduyile a madadin NMA ya fito Ranar Lahadi ya na kira ga gwamnatin tarayya ta dauki mataki na musamman na gyara sha’anin kiwon lafiya, ba tare da wani bata lokaci ba.

DUBA WANNAN: Ministan kasafin kudi ya yi magana a kan gobarar ofishin babban akanta na kasa

NMA ta koka da yadda gwamnatin Buhari ta yi watsi da ita wajen daukar matakan da ya kamata a bi wajen shawo kan cutar Coronavirus, amma kuma ake gayyatar mutanen kasar Sin.

Dr. Faduyile ya ke cewa: “An yi katari, yawan mace-macen da aka samu a kasar Italiya ya karu sosai a daidai lokacin da Likitocin Sin su ka shiga kasar da sunan sun je bada gudumuwa.”

“Ko majalisar dinkin Duniya ta yabawa kokarin da Najeriya ta ke yi. Kin yabawa kokarin Malaman asibitinmu na gida ne a ce a wannan lokaci an gayyato Likitocin Sin,” Inji Faduyile.

Ita ma TUC ta bakin shugabanta da Sakatare na kasa, Quadri Olaleye da Musa Lawal-Ozigi sun ce ganin yadda ake fama da karancin masu cutar COVID-19, babu bukatar a kira Sinawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel