Annobar Corona: An yafe ma mutanen dake zaman gidajen haya kudi haya na watanni 3

Annobar Corona: An yafe ma mutanen dake zaman gidajen haya kudi haya na watanni 3

Yan haya da dama a kasar Kenya za su samu sauki yayin da kungiyar masu gidajen haya da yan haya ta kasar, LATAK, ta yafe musu kudin hayan watanni uku sakamakon bullar annobar Corona virus mai toshe numfashi a kasar.

Daily Trust ta ruwaito a yanzu haka kasar Kenya na da mutane 172 da suka kamu da cutar, inda mutane shida suka mutu yayin da mutane 7 ne kacal suka warke daga cutar, hakan tasa kungiyar LATAK ta bullo da wannan tsari.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Yan majalisun Kaduna sun bayar da makudan kudade don taimaka ma jama’a

Annobar Corona: An yafe ma mutanen dake zaman gidajen haya kudi haya na watanni 3
Shugaban kenya
Asali: Twitter

Kungiyar ta umarci dukkanin masu gidajen haya su yafe ma yan hayansu kudin haya na watanni uku farawa daga watan Afrilu, Mayu zuwa Yuni, haka zalika ta yi kira ga gwamnati ta umarci bankuna su daga ma masu gidajen haya kafa daga biyan basussukan da suka amsa na tsawon watanni 6.

Kungiyar ta nemi gwamnatin kasar ta gaggauta dabbaka wadannan matakai a matsayin wasu hanyoyon sassauta ma jama’a mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki a sanadiyyar barkewar annobar Coronavirus a kasar.

Mista Michael Munene, wani mamalakkin gidajen haya a yankin Nyandrua na kasar Kenya ya sha jinjina daga jama’a bayan ya sanar da yafe ma yan hayansa kudin haya na tsawo watanni biyu, tun daga nan masu gidajen haya suka bi sawunsa suna koyi da shi.

Shi ma shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya nemi masu gidajen haya su rage farashin gidajensu domin yan hayansu su samu sauki duba da matsanancin halin rashin kudi da jama’a suka afka a sanadiyyar Corona.

A wani labarin kuma, shugaban kasar Afirka ta kudu, Mista Cyril Ramaphosa ya dakatar da ministar sadarwa, Stella Ndabeni Abrahams, na tsawon watanni 2 sakamakon kamata da aka yi da laifin karya dokar hana shige da fice da zirga zirga a yayin marran annobar Coronavirus.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito fadar shugaban kasar Afirka ta kudu ta bayyana daga cikin watanni biyu da shugaba Ramaphosa ta dakatar da Stella, ba za’a biyata albashin wata daya ba.

Mai magana da yawun shugaba Ramaphosa, Khusela Diko ta bayyana cewa: “Game da zargin da ake yi ma minista cewa ta yi ma dokar hana zirga zirga karan tsaye kuwa, gwamnati ta yanke shawarar kyale doka ta yi aikinta a kan ta.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng