Allah Ya kubutar da hadimin gwamnan jahar Nassarawa daga hannun masu garkuwa

Allah Ya kubutar da hadimin gwamnan jahar Nassarawa daga hannun masu garkuwa

Allah Ya kubutar da babban mashawarcin gwamnan jahar Nassarawa Abdullahi Sule a kan harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya, John Mamman, daga hannun miyagu yan bindiga da suka yi awon gaba da shi.

Daily Trust ta ruwaito wani dan uwan Mamman da ya nemi a sakaya sunansa ne ya tabbatar da tsirarsa, inda yace a daren Talata masu garkuwan suka sako shi.

KU KARANTA: Za mu dawo da yan Najeriya, amma sai sun yi gwajin Coronavirus – hadimar shugaban kasa

Allah Ya kubutar da hadimin gwamnan jahar Nassarawa daga hannun masu garkuwa
Allah Ya kubutar da hadimin gwamnan jahar Nassarawa daga hannun masu garkuwa
Asali: Facebook

Idan za’a tuna, yan bindiga sun yi awon gaba da John Waje Mamman ne a gidansa da ke garin Dari a karkashin karamar hukumar Kokona a daren ranar Asabar.

Wani shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa Mamman yana tare da abokansa a lokacin da 'yan bindiga suka kutsa cikin gidan suka tafi da shi, ya kara da cewa 'yan bindigar, sun kewaye gidan Mamman tare da yin harbin iska domin tsorata jama'a, amma duk da haka jama’a sun kama guda daga cikinsu.

Kwatsam kuma sai a ranar Talata aka samu rahoton yan bindigan sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 20 kafin su sake shi tare da bukatar a saki daya daga cikin mambobinsu da jami’an tsaro suka kama ko kuma su kashe Mamman.

Wata majiya ta kusa da ahalinsa ta ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci naira miliyan 150 ne da farko, inda daga bisani suka rage zuwa naira miliyan 20, Ko cewa a lokacin da masu garkuwan suka magana da iyalansa, iyalan sun jiyo muryar Mamman, yana rokon afuwa.

Ita ma rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Nassarawa ta tabbatar da lamarin, kamar yadda kaakakinta, ASP Rahman Nansel ya bayyana, amma babu wani tabbacin ko an biya kudin fansar ko kuma akasin haka.

A wani labarin kuma, Yayan gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, watau Yaya Adamu ya kubuta daga hannun miyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane bayan kwashe kwanaki 12 a hannunsu.

Jaridar The Nation ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, DSP Kamal Abubakar ne ya bayyana haka ga manema labaru da daddaren Talata, 7 ga watan Afrilu. Sai dai bai bayyana ko an biya kudin fansa kafin a sako Yaya Adamu ba, ko kuwa a’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel