Kano: Hukuma ta haramta nuna fim din kwana casa'in

Kano: Hukuma ta haramta nuna fim din kwana casa'in

- Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a karkashin shugabancin Isma'il Na'Abba Afakalla ta dakatar da haska shirin Kwana casa'in da Gidan Badamasi

- Hukumar tana zargin cewa an dau wani sashin fim din na kwana casa'in inda aka rungume wata a cikin wani sashi na kantin siyar da kaya

- Amma kuma gidan talabijin din ya ce ba za a daina haska fina-finan ba don hukumar ba ta da hurumin wani iko da su

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a karkashin shugabancin Isma'il Na'Abba Afakalla ta ba gidan talabijin mai zaman kanshi na Arewa 24 umarnin dakatar da haska fina-finan Kwana Casa'in da Gidan Badamasi.

Ta basu wa'adin sa'o'i 48 ne don tabbatar da an dena haska su saboda sun taka dokar jihar Kano.

Kamar yadda wani sashi na takardar da hukumar ta aika wa gidan talabijin din ta bayyana, ta ce ta dauka wannan matakin ne saboda wani sashi na fim din kwana casa'in din ya saba wa al'adar jama'ar jihar Kano.

Akwai wani sashi da aka nuna a shirin makon da ya gabata, inda aka nuna wani mutum ya rungumi wata a cikin wani kantin sayar da kaya na Sahad Stores da ke Kano.

Kano: Hukuma ta haramta nuna fim din kwana casa'in
Kano: Hukuma ta haramta nuna fim din kwana casa'in
Asali: Instagram

KU KARANTA: Mamaki da al'ajabi: Buhari ya bayyana na hannun daman Jonathan a matsayin dan takarar sanatan APC

Kamar yadda jaridar Daily Trust Aminiya ta ruwaito, hukumar ta ce tana da alhakin dubawa tare da tantance duk wani fim da aka shirya da Hausa.

A don haka ne take bukatar cewa duk wani fim din na kwana casa'in da za a kara haskawa, sai ta tace.

Kamar yadda daya daga cikin marubutan fim din kwana casa'in da gidan Badamasi, Nazir Adam Salih yace, hukumar tace fina-finai ba ta da wata alaka da gidan talabijin din.

Don haka bata da hurumin hana su haska fina-finansu. Za su ci gaba da haskawa duk da wasikar bukatar dakatar da hakan ta riskesu.

Ya ce a matsayinsu na Musulmi kuma Hausawa, suna iya kokarinsu wajen kare martabar addininsu kuma za su kiyaye duk wani abu da zai iya kawo matsala ta wannan bangaren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel