Ayi watsi da kasafin 2020, a rage kudin Majalisa da fadar shugaban kasa - Atiku

Ayi watsi da kasafin 2020, a rage kudin Majalisa da fadar shugaban kasa - Atiku

A lokacin da ake tunanin yadda za a shawo kan annobar COVID-19, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya fadawa gwamnatin tarayya ta yi watsi da kasafin kudin 2020.

Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta shirya wani sabon kundin kasafin kudi da zai fitar da Najeriya daga cikin kangin Coronavirus da ta samu kan ta a halin yanzu.

Atiku Abubakar ya fitar da wannan jawabi ne ta ofishinsa na yada labarai. Ganin yadda kasuwa ta juya, Atiku ya ke cewa: “Lissafin farashin danyen gangar man da mu ka yi ya saki layi.”

Jawabin na Atiku ya ke cewa: “A dalilin haka ba mu da karfin da za mu yi wa ‘Yan majalisarmu kasafin fiye da Naira biliyan 100 da kuma kusan Naira biliyan ga fadar shugaban kasa.”

‘Dan siyasar ya bayyana cewa Najeriya ba ta taba samun sukunin da za ta rika batar da wadannan makudan kudi ba, ya nuna cewa karambani ne kurum gwamnatin tarayya ta ke yi.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus ta ci Mutum daya a Garin Shugaban kasa

Ayi watsi da kasafin 2020, a rage kudin Majalisa da fadar shugaban kasa - Atiku

Atiku ya fadawa Gwamnatin Najeriya cewa cin bashi ba mafita ba ce
Source: Twitter

“Meyasa gwamnati ta ke saurin ta ruga ta karbi aron kudi a duk lokacin da ta samu dama? Ya nuna lalaci da rashin nuna kishi da sadaukar da kai domin shawo kan tattalin kasar.”

“Ba za mu cigaba da karbo bashin tulin kudi ba a daidai lokacin da jami’ai su ke karbar sababbin motoci daga kasashen waje. Ba za a rika mana kallon kirki idan ba mu rage facaka ba.”

Idan ba ku manta ba a cikin kwanakin baya ne aka fara rabawa ‘Yan majalisa sababbin motoci kirar Toyota Camry na shekarar 2020 a daidai lokacin da ake fama da cutar COVID-19.

Wazirin Adamawa ya ce dole gwamnatin kasar ta nemi hanyar da za ta rage kashe dukiya a kan abubuwan da ba za su zama tilas ba, domin a iya daukar dawainiyar kasar a halin yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel