COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)

- Wasu mazauna Abuja da Legas sun fara karya dokar hana kaiwa da kawowa da gwamnatin tarayya ta saka musu

- Kamar yadda aka sani, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rufe jihohin a ranar 29 ga watan Maris don hana yaduwar cutar coronavirus

- Amma kuma mazauna jihohin sun bayyana cewa basu samun kayayyakin bukata don haka dole su fito tare da karya dokar

Wasu mazauna Abuja da Legas sun fara karya dokar hana walwala da gwamnatin tarayya ta bada don hana yaduwar cutar coronavirus a kasar nan.

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)
Source: Twitter

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)
Source: Twitter

A ranar 29 ga watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin kulle ga dukkan jama'ar jihohin Ogun, Legas da Abuja a matsayin hanyar hana yaduwar annobar coronavirus.

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)
Source: Twitter

Amma kuma, wasu daga cikin mazauna jihohin na korafi tare da koken wannan kulle da suke fuskanta. Sun nuna cewa basu samun abubuwan bukata na rayuwa, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Cutar Coronavirus na dawowa jikin mutanen da aka yi musu magani, yayin da ta dawo jikin mutane 51 da suka warke a kasar Koriya ta Kudu

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta zagaya lunguna da sako na birnin tarayya Abuja da kuma Legas don ganin yadda ake bin dokar. A yayin da aka hana masu ababen hawa kaiwa da kawowa, sauran da suke da manyan uziri ana barinsu yawo cikin garin.

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)
Source: Twitter

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)

COVID-19: Yadda jama'a suka yi watsi da doka a Abuja da Legas (Hotuna)
Source: Twitter

A wani labari na daban, shugabannin cibiyoyin lafiya na kasar Koriya ta Kudu sun bayyana cewa kwayar cutar coronavirus na iya suma a jikin dan Adam sannan ta sake tashi bayan kwanaki.

Sun sanar da hakan ne kuwa bayan mutane 51 da suka warke daga cutar sun sake bayyana da ita bayan kwanaki kadan da aka sallamesu daga asibiti. Majinyatan, wadanda suke daga yankin Daegu, an killace su ne bayan an gano suna dauke da cutar a karo na biyu, kamar yadda shagin Linda Ikeji ya wallafa.

Kamar yadda cibiyar kula da cutuka masu yaduwa ta kasar Koriya din ta bayyana, majinyatan dai sun fito ne daga sashin kasar da cutar ta fi yi wa illa. An kuma killace su ne kuma ana zargin kwayar cutar ta sake tashi ne bayan an kasheta daga jikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel