Sakamakon gwajin mutane 2 da ake zargi da corona a Taraba ya fito

Sakamakon gwajin mutane 2 da ake zargi da corona a Taraba ya fito

Gwamnatin jihar Taraba ta ce sakamakon gwajin cutar covid-19 da aka gudanar a kan wasu 'yan asalin jihar mutum biyu ya nuna cewa basa dauke da kwayar cutar.

Kwamishinan lafiya a jihar sannan shugaban kwamitin kwararru a kan annobar covid-19, Innocent Vakkai, ne ya sanar da hakan ranar Talata a Jalingo yayin da ya ke gabatar da jawabi ga manema labarai a kan kokarin gwamnati na dakile yaduwar cutar.

Ya ce sakamakon gwajin mutane biyun da aka aika ya nuna cewa basa dauke da kwayar cutar covid-19.

"Ba mu da mai dauke da kwayar cutar coronavirus a jiharmu, kuma muna fatan za mu dore a hakan," a cewarsa.

Ya ce gwamntin jihar ta raba sinadarin tsaftace hannu da sauran kayan kare kai ga cibiyoyin duba lafiya da asibitocin da ke jihar.

Mista Vakkai ya yi kira ga masu arziki da sauran masu hannu da shuni da su bayar da tallafin domin taimakon kokarin gwamnatin jihar.

Kazalika, ya bukaci mazauna jihar da su cigaba da biyayya ga dokokin kare kai, musamman nesantar juna, da kuma kula tsaftace hannu da sabulu a kai - a kai domin dakile yaduwar kwayar cutar.

Sakamakon gwajin mutane 2 da ake zargi da corona a Taraba ya fito
Sakamakon gwajin mutane 2 da ake zargi da corona a Taraba ya fito
Asali: UGC

Gwamnatin jihar Taraba ta rufe iyakokinta, ba shiga, ba fita, tare da hana taron jama'ar da yawansu ya kai 20 a fadin jihar.

A jiya, Litinin ne cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta tabbatar da cewa sabbin dakunan gwajin kwayar cutar covid-19 a jihohin Kano, Kaduna, Filato da Maiduguri za su fara aiki a cikin satin nan.

DUBA WANNAN: Covid-19: Lokacin da 'yan Najeriya za su fara faduwa suna mutuwa yana nan tafe - Farfesa Usman

Dakunan gwajin za su taimaka matuka wajen shawo kan yaduwar kwayar cutar covid-19 ta hanyar gano masu dauke da kwayar cutar ba tare da bin doguwar hanya ba.

Bashir Ahmad, mataimaki na musamman ga shugaba Buhari a bangaren kafafen sadarwa na zamani, ne ya sanar da hakan a cikin wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin tuwita a daren ranar Litinin.

Kafin sanar da lokacin fara aikin cibiyoyin, akwai wasu cibiyoyi biyar a jihohin Najeriya uku da ke gudanar da gwajin kwayar cutar covid-19 a kan wadanda ake zargin sun kamu da kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel