Covid-19: Lokacin da 'yan Najeriya za su fara faduwa suna mutuwa yana nan tafe - Farfesa Usman

Covid-19: Lokacin da 'yan Najeriya za su fara faduwa suna mutuwa yana nan tafe - Farfesa Usman

Batun kunnen uwar shegu da nuna halin 'ko in kula' da jama'a ke yi a kan sharwarar masana da biyayya ga matakan gwamnati domin kare kai daga kamuwa da cutar covid-19 ya fara saka damuwa a zukatan kwararru a harkar lafiya a Najeriya.

Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya nuna damuwarsa tare da bayyana cewa abinda suke gani a matsayinsu na kwararru yana matukar tayar musu da hankali

A cewar tsohon shugaban na NHIS, annobar cutar covid-19 za ta iya yin mummunar barna a Najeriya matukar jama'a basu yadda suke wasarairai da matakan kare kai daga kamuwa da cutar ba.

A hirar da ya yi da sashen Hausa da rediyon BBC, Farfesa Usman, hankalin likitocin Najeriya har ma da na kasashen ketare a tashe yake saboda ganin annobar cutar da ta fara daga kasar China, inda ta kashe dumbin mutane, yanzu ta bazu zuwa kowanne yanki na duniya.

"Dubi yadda cutar ta yi barna a Italy, ta shiga Ingila har ta kai ga yanzu an kwantar da shugabansu a asibiti saboda yana dauke da wannan cuta.

Covid-19: Lokacin da 'yan Najeriya za su fara faduwa suna mutuwa yana nan tafe - Farfesa Usman

Farfesa Usman Yusuf
Source: UGC

"Ta shiga kasar Amurka sai barna take yi duk kudinta da bama-bamanta. Mutane sai mutuwa suke yi inda ake mayar da filayen wasa asibiti.

"Amma mu a nan Najeriya, jama'a basu dauki cutar da muhimmancin da ya kamata ba, hakan ya tashi hankalinmu, musamman yadda muke jin jama'a na cewa ba ta zo arewa ba, ai ba ta kawo nan ba," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Rabawa talakawa shinkafa, daukan ma'aikata 774,000 da sauran matakan rage radadi 7 da FG ta dauka

Sanna ya cigaba da cewa, "duk maganganun nan ba gaskiya bane, duk kasashe akwai lokacin da kwayar cutar ke bunkasa idan jama'a basu bayar da goyon ba.

"Idan jama'a basu fahimta ba haka za mu cigaba da abubuwa, mutane suna faduwa suna mutuwa."

Kazalika ya bayyana cewa, kar jama'a su yi kuskuren tunanin cewa iyakar mutanen da aka sanar ne kadai ke dauke da kwayar cutar. Ya kara da cewa, "ai ba za a san iya adadin masu dauke da kwayar cutar ba sai an bincika. Mu na zama ne kawai mu na cewa ai Legas ne da Ogun kawai, shikenan sai a kwanta a cigaba da zuwa Masallaci ana yi wa juna tari, ana zuwa kasuwanni, ana shiga motocin haya, ana cigaba da cewa ai ciwon Abuja ne, ai ciwon Legas ne", wanda a cewar Farfesan, "sam hakan ba gaskiya bane".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel