'Yan sanda sun kama ango da amarya da sauran 'yan biki da suka karya dokar hana fita da gwamnati ta saka

'Yan sanda sun kama ango da amarya da sauran 'yan biki da suka karya dokar hana fita da gwamnati ta saka

- Rundunar 'yan sandan kasar Afrika ta Kudu ta damke ango, amarya, fasto da kuma 'yan biki a kalla 40

- Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa, sun yi hakan ne sakamakon take dokar walwala da gwamnatin kasar ta saka

- Kamar yadda jami'in hulda da jama'a na kasar ya bayyana, za a gurfanar dasu a gaban kotu nan ba da jimawa ba don karbar hukuncinsu

Rundunar 'yan sandan kasar Afrika ta Kudu (SAPS) ta damke ango da amarya, fasto da kuma sama da 'yan biki 40 sakamakon karya dokar hana walwala ta kasar da suka yi. An kama su ne yayin da suke shagalin biki a Richard Bay, wani gari da ke KwaZulu-Natal.

'Yan sandan sun yi kamen ne yayin da ake tsaka da bikin kuma an tasa keyar mutanen ne zuwa ofishin 'yan sanda na Empangeni.

'Yan sanda sun kama ango da amarya da sauran 'yan biki da suka karya dokar hana fita da gwamnati ta saka

'Yan sanda sun kama ango da amarya da sauran 'yan biki da suka karya dokar hana fita da gwamnati ta saka
Source: Facebook

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar, Birgediya Vishnu Naidoo wanda ya tabbatar da kamen, ya ce masu gurfanarwar ne za su sanar da 'yan sandan hukuncin mutanen.

KU KARANTA: Asibitocin mu sun cika babu inda zamu saka ku - Martanin kasar Amurka ga mutanenta na Najeriya da suke son komawa gida

Naidoo ya ce: "Mutane na daukar komai da wasa. Basu duban hatsarin muguwar cutar. A halin yanzu, bana tunanin akwai dalilin tara jama'a don yin taron biki. Za mu tattauna da dukkansu don jin dalilin take doka.

"Za mu yanke musu hukunci don sun take doka wanda hakan ke da matukar hatsarin gaske. Masu gurfanarwar ne za su bayyana mana hukuncin da ya dace. Bana tunanin za mu bukaci wani bayani daga wajensu don kuwa sai mun zanta da babban jami'in gurfanarwa."

Ana tsammanin wadanda suka take dokar za su bayyana a gaban kotu nan da ranar 6 ga watan Afirilu.

A ranar 26 ga watan Maris na 2020 ne gwamnatin kasar Afirika ta Kudu ta bayyana dokar hana walwala ta kwanaki 21. Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya ce hakan ya zama dole don gujewa masifa da annoba. Ya kuma umarci rundunar sojin kasar da su tabbatar da an bi dokokin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel