Covid-19: Buhari ya amince da daukar ma'aikata 774,000
- Ministar kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da daukar 'yan Najeriya 774,000 aiki
- Ministar ta bayyana cewa, shugaban ya amince da hakan ne sakamakon illar da annobar coronavirus tayi a kasar nan
- A cewarta, za a diba mutane 1,000 a kowacce karamar hukuma cikin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar nan
Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da daukar 'yan Najeriya 774,000 a cibiyar ayyuka na musamman a kasar nan don tallafi a kan illolin annobar coronavirus.
Zainab Ahmed ta bayyana hakan ne a taron manema labarai da ta gudanar don bayyana irin girgizar tattalin arziki da annobar coronavirus tayi wa kasar nan a ranar Litinin a Abuja.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Labari da dumi-dumi: Tsohon malamin da ya koyar da Abacha, Dr Habibu Gwarzo ya rasu a Kano
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, za a diba mutane 1,000 ne daga cikin kananan hukumomi 774 na fadin kasar nan.
Kamar yadda tace, an ware Naira biliyan 60 domin tallafi da kuma alawus sakamakon barkewar annobar coronavirus a kasar nan.
Ta ce da farko dai Buhari ya amince da tada cibiyoyin ayyuka na musamman a jihohi 8 na kasar nan. Ta kara da cewa Buhari ya amince cibiyoyin su taba dukkan jihohi 36 tare da birnin tarayya na kasar nan.
Kuma za su fara aiki ne kafin lokacin daminar shekarar nan.
A wani labarin, kun ji cewa kwamishinan Lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya ce jihar ta gama shirye-shiryen fara gwajin maganin COVID-19 a kan majiyanta a jihar tare da hadin gwiwar Cibiyar kawar da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) da wasu hukumomin.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata jawabi da ya yi a ranar Litinin kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Farfesa Abayomi ya ce wasu kasashen duniya suma sun fara gudanar da irin wannan gwaje-gwajen a asibitoci da cibiyoyin lafiya da niyyar gano takammamen maganin da za a rika amfani da shi domin maganin covid-19.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng