COVID-19 ta fara yaduwa tsakanin junan ‘Yan Najeriya – Minista

COVID-19 ta fara yaduwa tsakanin junan ‘Yan Najeriya – Minista

Tun kwanakin baya gwamnatin Najeriya ta dauki matakin garkame iyakokinta da kuma rufe duk filayen sauka da tashin jiragen sama domin hana yaduwar cutar COVID-19.

Duk da haka ana samun masu dauke da wannan cuta ta Coronavirus, wanda hakan ya nuna akwai matukar yiwuwar cewa COVID-19 ta na yawo tsakanin ‘Yan kasar a cikin gida.

Ministan lafiya watau Dr. Osagie Ehanire ya nuna wannan alamu tun a makon da ya gabata. Ganin yadda ake samun karuwar cutar, Ministan ya ce ta na yawo tsakanin ‘yan kasa.

Ministan na Najeriya, Osagie Ehanire, ya fara yin wannan bayani lokacin da ya ke wani jawabi a lokacin da aka gayyace shi a gidan talabijin na TVC a Ranar Alhamis da ta gabata.

Ehanire ya ke cewa mutane su na kamuwa da wanan cuta ba tare da sun fita Najeriya ba, sai da ta hanyar haduwa da wani da ba a san cewa ya na dauke da kwayar cutar a jikinsa ba.

KU KARANTA: Likitoci sun gano COVID-19 a jikin wata Damisa a Amurka

COVID-19 ta fara yaduwa tsakanin junan ‘Yan Najeriya – Minista
Akwai bukatar a daina shiga bainar Jama'a domin takaita yaduwar COVID-19
Asali: Facebook

Bayan an samu masu dauke da kwayar cutar COVID-19 a Osun da Ekiti, maganar yaduwar cutar tsakanin ‘Yan kasa ta kara karfi. Wannan ya sa aka kara kiran a rage shiga Jama’a.

Kwamishinan lafiyan jihar Legas, Dr, Akin Abayomi, ya tabbatarwa ‘Yan jarida wannan kwanaki a lokacin da su ka zanta, ya ce babu shakka cutar ta na yawo a cikin gida a Legas.

Su ma Likitocin Najeriya sun bayyana cewa wannan cuta mai kawo wahalar numfashi ta na yawo tsakanin mutanen gida bayan ganin yadda cutar ta ke kara yaduwa a kasar.

Kamar yadda BBC Hausa ta bayyana, Likitocin kasar a karkashin kungiyarsu ta NMA, sun nuna rashin goyon bayan gayyatar da Najeriya ta yi wa Malaman asibiti daga kasar Sin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng