Tsohuwar Pep Guardiola ta mutu bayan ta kamu da cutar COVID-19
Kasar Sifen ta na cikin kasashen da su ka fi kowane gamuwa da munin annobae cutar COVID-19. Kawo yanzu akalla mutum 135, 000 ne su ka kamu da wannan cuta a kasar ta Turai.
Ana tsakiyar wannan yanayi ne sai rahotanni su ka fito cewa Mahaifiyar babban Mai horas da ‘Yan kwallon kafan kungiyar Manchester City, Pep Guardiola ta mutu a sanadiyyar cutar.
Kungiyar Manchester City ta Ingila ta bada sanarwar cewa tsohuwar Koci Pep Guardiola ta mutu bayan ta kamu da wannan cuta. Dolors Sala Carrió ta bar Duniya ne ta na shekara 82.
Marigayiya Dolors Sala Carrió ta rasu ne a Garin Manresa da ke cikin Garin Barcelona a kasar Sifen. Kungiyar kwallon kafan ta bayyana cewa ta ji zafin wannan rashi da aka yi.
Man City ta fitar da wannan jawabi ne a shafin Tuwita a Ranar 6 ga Watan Afrilu, 2020. Kungiyar ta ce: “Kowanenmu da ke da alaka da wannan kungiya ya na mika ta’aziyyarsa”
KU KARANTA: ‘Dan wasan Man City da ya cashe da karuwai zai yabawa aya zaki
Kungiyar ta kuma mika ta’aziyya ga Iyali da sauran ‘Yanuwa da Abokan arzikin kocin. City ta dauko hayar Pep Guardiola ne a 2016 bayan ya rabu da kungiyar Bayen Munchen.
Shi ma shugaban kungiyar kwallon na Manchester, Sheikh Khaldoon Al Mubarak ya fito ya yi magana a shafinsa na Tuwita ya na mai yi wa Pep Guardiola ta’aziyyar wannan rashi.
“Mu na mika addu’o’inmu da jimami ga Pep (Guardiola) da Iyalinsa a wannan lokaci mai cike da ban takaici. Shi da Iyalinsa su na da goyon baya da kaunar daukacin kungiyar.”
Kungiyoyi irinsu Manchester United Liverpool, da Everton sun aikawa Mutumin Kataloniyar ta’aziyyarsu. Mutane fiye da 13, 000 cutar COVID-19 ta kashe yanzu a kasar Sifen.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng