Yanzu Yanzu: Wani kwamishinan Taraba ya mutu

Yanzu Yanzu: Wani kwamishinan Taraba ya mutu

- Kwamishinan alkarya da wutar lantarki na jahar Taraba, Alexenda Markus Senlo ya rasu

- An tattaro cewa Senlo ya rasu ne a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu bayan dan gajeren jinya

- Marigayin ya kasance tsohon shugaban karamar hukuma a jahar

Rahotanni da muke samu yanzu ya nuna cewa Kwamishinan birane da wutar lantarki na jahar Bayelsa, Alexander Markus Senlo ya rasu.

Senlo ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya na dan wani lolaci kadan, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Wani kwamishinan Taraba ya mutu

Yanzu Yanzu: Wani kwamishinan Taraba ya mutu
Source: Twitter

Senlo wanda ya kasance tsohon shugaban karamar hukuma kuma kwashina sau biyu ya rasu ne a asibitin Yola.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi sama da fadi kayan tallafin da gwamnati ta tanadar ma jama’a

A wani rahoto na daban, mun ji cewa 'Yan bindiga sun yi awon gaba da John Waje Mamman, mai bawa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, shawara a kan kananan hukumomi da raya karkara.

An sace Mamman a gidansa da ke garin Dari a karkashin karamar hukumar Kokona a daren ranar Asabar.

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa manema labarai cewa Mamman yana tare da abokansa a lokacin da 'yan bindiga suka kutsa cikin gidansa suka tafi da shi.

Ya bayyana cewa 'yan bindigar, wadanda aka gano cewa masu garkuwa da mutane ne, sun kewaye gidan Mamman tare da yin harbin iska domin tsorata jama'a.

Shaidar ya bayyana cewa, sa'a ta kwacewa daya daga cikin 'yan bindigar a yayinda wasu matasa suka yi zafin nama suka damke shi.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kakakin rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, ya ce, "har yanzu babu wanda ya sanar da ofishin rundunar 'yan samu batun sace mai bawa gwamnan shawara."

Har wa yau rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani kasurgumin dan bindiga mai garkuwa da mutane a jahar Katsina mai suna Abdulhadi Dan Nashe, kamar yadda jaridar Katsina Post ta ruwaito.

Majiyar ta kara da cewa dalilin wannan rashin fahimta da ya kunno kai a tsakanin yan bindigan baya rasa nasaba da wata tirka tirka da ta taso tsakanin Dan Nashe da matarsa, wanda ita kan kanwa ce ga wani shugaban yan bindiga, mai suna Dangote.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel