Annobar Coronavirus: Buhari ya zari dala miliyan 150 daga wani asusun Najeriya

Annobar Coronavirus: Buhari ya zari dala miliyan 150 daga wani asusun Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da cire dala miliyan 150, kimanin naira biliyan 55 daga asusun kasa na musamman wanda aka fi sani da suna ‘Sovereign Wealth Fund’.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban ya amince a cire kudin ne domin raba ma matakan gwamnatin tarayya, jahohi da kuma na kananan hukumomi sakamakon bullar annobar nan mai toshe numfashi, watau Coronavirus.

KU KARANTA: Buratai ya ce sun daina fallasa shirye shiryen da suka tanadar ma Boko Haram

Annobar Coronavirus: Buhari ya zari dala miliyan 150 daga wani asusun Najeriya
Annobar Coronavirus: Buhari ya zari dala miliyan 150 daga wani asusun Najeriya
Asali: Twitter

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare tsare, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka a ranar Litinin, a babban birnin tarayya Abuja yayin da take ganawa da manema labaru game da matakan da gwamnati take dauka don rage radadin Coronavirus.

Ministar ta bayyana cewa za’a cire kudaden ne don cike gibin da aka samu sakamakon karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwan duniya, inda tace tun daga watan Janairun kudaden shigar gwamnati ke yin kasa, wanda hakan ya shafi kudaden da ake rabawa tsakanin matakan gwamnatocin uku.

Haka zalika gwamnatin Najeriya za ta nemi karin kudaden bashi daga bankin lamuni na duniya, IMF, bankin duniya da kuma bankin cigaban nahiyar Afirka domin kulawa da matsalolin tattalin arzikin da za’a fuskanta sakamakon Coronavirus.

A makon da ta gabata ne shugaba kasa Buhari ya kafa wata kwamiti ta musamman da zata bashi shawara a kan tattalin arzikin Najeriya a karkashin jagorancin Ministar kudi, Zainab Ahmad, sauran mambobin sun hada da ministar man fetir, Timipire Sylva, gwamnan bankin Najeriya, Godwin Emefiele da shugaban NNPC, Mele Kyari.

A wani labarin kuma, an samu wasu miyagun yan bindiga a jahar Bayelsa da suka kwashe tarin kayan abinci da gwamnati tanadar ma jama’a talakawa da gajiyayyu a matsayin tallafi.

Wani shaidan gani da ido da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa miyagun sun afka wurin da ake rabon abincin ne dauke da bindigu inda suka dinga harbe harbe, wanda hakan yasa jama’a tserewa, kafa mai na ci ban baki ba.

Nan da nan bayan kowa ya tsere sai suka kwashi iya abin da zasu iya diba, suka kuma fice zuwa cikin wani daji, daga bisani masu rabon sun tabbatar da abincin da yan bindigan suka kwashe na karamar hukumar Sagbama, Ekeremor, da kudancin Ijawa ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel