Covid-19: Kayan duba lafiya da FG ta sayo daga Turkiyya sun iso Najeriya

Covid-19: Kayan duba lafiya da FG ta sayo daga Turkiyya sun iso Najeriya

A yayin hutun karshen mako ne gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da cewa ta karbi rukunin farko na kayan duba lafiya da ta sayo daga kasar Turkiyya domin dakilewa yaduwar annobar coronavirus tare da duba lafiyar wadanda suka kamu da cutar.

Wani jirgin sama ne, Boeing 777, mai lamba 5N-BWI, ya sauke kayan a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da daren ranar Asabar bayan ya kwaso su daga Istanbul ta kasar Turkiyya.

Jirgin ya tashi ne daga Najeriya da safiyar ranar Asabar, sannan ya dawo Najeriya a ranar tare da kayan da ya dauko daga kasar Turkiyya mai nisan tafiyar sa'o'i 7 daga Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jirgin zai sake tashi zuwa kasar China a ranar Litinin domin sake dauko wani rukuni na kayan aikin duba lafiyar jama'a.

Covid-19: Kayan duba lafiya da FG ta sayo daga Turkiyya sun iso Najeriya
Covid-19: Kayan duba lafiya da FG ta sayo daga Turkiyya sun iso Najeriya
Asali: Twitter

"Jirgin sama na 'Air Peace' zai sake kawowa gwamnatin tarayya wasu kayan da ta saya. Jirgin zai bar Najeriya a ranar Litinin domin fara bulaguron da babu tsayawa na sa'o'i 15," a cewar majiyar Daily Trust.

DUBA WANNAN: Covid-19: Trump ya yi wa Amurkawa mummunan albishir din abinda zai faru sati mai zuwa

Babban jami'in da ke kula da sarrafa jiragen kamfanin 'Air Peace', Toyin Olajide, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa kokarinta na shawo kan annobar cutar coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel