Tashin hankali: Mutane 3 da suka kamu da Coronavirus a Kaduna sun yi mu’amala da El-Rufai
Kafatanin ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Kaduna na zaman dar dar biyo bayan gano wasu mutane uku a jahar Kaduna da suka kamu da cutar Coronavirus sakamakon mu’amala da suka yi da gwamnan jahar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
Jaridar Guardian ta ruwaito a yanzu haka ma’aikatan fadar gwamnatin jahar, gidan Sir Kashim Ibrahim na cikin zulumi saboda rashin sanin matsayinsu, musamman ga wadanda suka mu’amalanci gwamnan sosai da sosai.
KU KARANTA: Alhaki dan kwikwiyo: Yaran yan bindiga sun juya ma jagoransu baya, sun kashe shi har lahira
Idan za’a tuna gwamnan da kansa ya sanar da kamuwarsa da cutar, kuma tun daga wannan lokaci ya killace kansa, inda yake samun kulawa da kwararrun likitoci, sai dai jami’an kiwon lafiya sun ki amincewa su bayyana inda aka killace sauran mutane ukun.
Kamar yadda hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta tabbatar, akwai mutane hudu dake dauke da Coronvirus a jahar Kaduna, gwamnan nan ne na farko sai kuma wasu mutane uku da hukumar bata bayyana sunayensu ba.
Sai dai wata majiya ta karkashin kasa daga fadar gwamnatin jahar ta tabbatar ma majiyar Legit.ng cewa akwai wasu manyan hadiman gwamnan da kuma ma’aikatansa na gida da aka gudanar ma gwajin.
Zuwa yanzu dai uwargidar Gwamna El-Rufai, Hadiza Isma ta bayyana sakamakon gwajin da aka mata, kuma ya nuna bata dauke da cutar, ita ma matar gwamnan ta biyu, Asiya ta bayyana nata sakamakon gwajin, kuma bata dauke da shi, kamar yadda shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar, Sani Abdullahi Dattijo shi ma baya dauke da cutar.
A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Katsina a karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari ta umarci kafatanin ma’aikatan gwamnati da su koma bakin aikinsu daga ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu.
Gwamnatin ta sanar da haka ne cikin wata wasika dake dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jahar, Alhaji Idris Usman Tune dauke da kwanan watan 5/04/2020, inda ta bayyana cewa ma’aikatan za su dinga zuwa aiki ne daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana.
Haka zalika gwamnatin ta yi kira ga ma’aikata da su kasance suna dabbaka ka’idar kauce ma shiga cunkoson jama’a, tsayawa nesa nesa da juna, wanke hannuwa da kuma amfani da sinadarin Sanitizer don tabbatar da an kare bullar COVID-19 a Katsina.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng