Jama’a za su rasa aikin yi a sakamakon barkewar cutar COVID-19

Jama’a za su rasa aikin yi a sakamakon barkewar cutar COVID-19

A daidai lokacin da ake takaicin mutanen miliyan daya sun kamu da cutar COVID-19 a Duniya. Mun fahimci za a ga tasirin wannan annoba sosai a Najeriya inda mutum 200 su ka kamu.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoton wani bincike da ta yi, wanda ya nuna cewa akwai alamun tattalin arzikin Najeriya zai shiga cikin wani mawuyacin hali a sakamakon annobar COVID-19.

Kawo yanzu dai COVID-19 ta durkusar da tattalin arzikin manyan kasashe irinsu Amurka da Birtaniya. A kasar Amurka mutane fiye da 700, 000 su ka rasa aikinsu a Watan jiya na Maris.

Duk da cewa babu alkaluman da ke nuna adadin mutanen da ke rasa aikinsu a Najeriya, hukumar NBS ta fitar da rahoto a bara da ke nuna cewa rashin aikin yi ya karu a kasar nan zuwa 23.1%.

Akalla mutane miliyan 20 ne ba su da abin yi wa Najeriya. Kuma akwai yiwuwar lamarin ya kara tabarbarewa a sakamakon annobar cutar Coronavirus kamar yadda Masana tatali su ke hange.

KU KARANTA: Abin da ya sa Shugaban Amurka bai rufe fuskarsa da tsumma

Jama’a za su rasa aikin yi a sakamakon barkewar cutar COVID-19

Masu aikin otel da kamfanonin jiragen sama sun fara ganin haza
Source: Twitter

Wani fitaccen Masanin tattalin arziki a Najeriya, Tope Fasua, ya bayyana cewa dokar ta-baci da gwamnati ta sa wajen rufe Garuruwan Legas da Abuja zai yi wa tattalin arzikin Yankin illa.

Akwai yiwuwar kasuwancin da su ka tsaya cak su gamu da cikas a wadannan manyan Birane. Haka zalika Tope Fasua ya ce masu shigo da kaya daga kasar waje su na fuskantar barazana.

Masanin ya shaidawa Jaridar cewa nan ba da dadewa ba Najeriya za ta shiga irin halin da aka shiga a kasar waje. Masu aiki a kamfanonin jiragen sama da sana'ar otel za su fi shiga matsi.

A dalilin haka ne hukumar IMF mai bada lamuni ta yi hasashen cewa tattalin arzikin Duniya zai tsuke da kimanin 12% a bana. Har yanzu dai Masana ba su kai ga gano maganin COVID-19 ba.

Bayan matsalar cikin gida, a kasuwannin Duniya abubuwa su na cigaba da cabewa Najeriya inda farashin gangar danyen mai ya karye raga-raga. Man ya yi arahan da bai taba yi bavtun 2002.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel