Covid-19: Sauyawar sakamakon gwaji a UBTH ya jefa tsoro a zukatan ma'aikata da jama'a

Covid-19: Sauyawar sakamakon gwaji a UBTH ya jefa tsoro a zukatan ma'aikata da jama'a

- Ma'aikatan lafiya da jama'a a Benin sun shiga halin firgici bayan wasu an samu kwayar cutar covid-19 a jikin wasu mutane da sakamakon gwajin farko ya nuna cewa basa dauke da kwayar cutar

- Daya daga cikin mutanen yana daga cikin masu dauke da cutar covid-19 da ake zargin cutar ta kashe Najeriya

- Bincike ya nuna cewa mai dauke da kwayar da ya mutu a UBTH, yana fama da matsanancin ciwon koda

An samu rudani da firgici a cibiyar gudanar da gwaji da killace masu dauke da kwayar cutar covid-19 da ke asibitin koyarwa na jami'ar Benin (UBTH) sakamakon sauyawar sakamakon gwajin wasu masu dauke da kwayar cutar coronavirus.

A ranar juma'a ne cibiyar shawo kan cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar da cewa wasu mutane biyu da ke dauke da kwayar cutar covid-19; daya a Legas, daya a Benin, sun mutu ba tare da bayar da karin bayani ba, lamarin da ya saka jama'a cikin fargaba a Benin.

Jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa sakamakon gwajin farko da aka gudanar a kan wasu mutane ya nuna cewa basa dauke da kwayar da cutar, amma sakamakon gwajin da aka maimaita ya nuna cewa suna dauke da kwayar cutar.

Covid-19: Sauyawar sakamakon gwaji a UBTH ya jefa tsoro a zukatan ma'aikata ta jama'a
Dakin gwajin Covid-19
Asali: Facebook

Tun bayan gwajin farko daka gudanar a kan mutanen, kungiyar likitocin asibitin (NARD) ta bayar da shawarar a mayar da su cibiyar killacewa a ranar 31 ga watan Maris, bisa zargin cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Gwamnatin Kano ta bude shafin yanar gizo na daukan ma'aikatan lafiya

Babban darektan likitocin asibitin UBTH, Farfesa Darlington Obaseki, ya bukaci jama'a su kwantar da hankalinsu tare da basu tabbacin cewa babu abinda zai gagari likitocin a kokarinsu da shawo kan annobar cutar.

A jawabin da hukumar asibitin ta fitar, ta bayyana cewa masu dauke da kwayar cutar da sakamakon nasu ya zo da rudani, suna fama da wasu sauran cututtukan kamar yadda sakamakon wasu gwaje-gwajen da aka yi musu ya nuna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel