Mutane 7 kacal suka halarci daurin auren diyar gwamnan Jigawa (Hotuna)

Mutane 7 kacal suka halarci daurin auren diyar gwamnan Jigawa (Hotuna)

Mutane bakwai kacal suka halarci taron gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, inda ya aurar da diyarsa ranar Asabar yana mai biyayya ga dokokin hana yaduwar cutar Coronavirus.

Hadimin gwamnan kan sabbin kafafan yada labarai, Auwal Sankara, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki inda yace a daura auren a jihar Kano.

Yace: "Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a Yau ya bada auren yar dan uwansa a yayin da yake kula da ka’idojin da aka kafa na samar da tazara tsakanin jama’a da kuma kayyade yawan masu halartar daurin aure zuwa mutane tara.

Daurin auren wanda akayi a gidan Gwamnan dake birnin dabo ya zama sanadin zamantowar Umar Murtala Adamu da Naseeba Badaru Abubakar a matsayin ango da amarya ba tare gayyar jama’a ba.

A baya bayannan Gwamnatin Jihar ta bada umarnin dakatar da duk wani biki illa dai duarin aure wanda shima aka kayyade zuwa mutane uku uku za suzo daga iyalan ango da amarya a matsayin wakilai sai kuma madaura auren.

Gwamnan ya kasance ya na mai kula da hakanne a wajen daurin auren danginsa domin jama’a suyi koyi.

Ku tuna, riga kafin wannan annobar itace kula da tsafta musamman wanke hannaye akai akai, da kuma samar da tazara tsakanin juna."

Hotuna:

Mutane 5 kacal suka halarci daurin auren diyar gwamnan Jigawa (Hotuna)

Mutane 5 kacal suka halarci daurin auren diyar gwamnan
Source: Facebook

Mutane 5 kacal suka halarci daurin auren diyar gwamnan Jigawa (Hotuna)

Mutane 7
Source: Facebook

A bangare guda, Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce gwamnati ba zata bayar da gawawwakin wadanda suka mutu sakamakon cutar Coronavirus ga iyalansu domin birnesu ba.

Ya ce ma'aikatar kiwon lafiya za ta birne saboda ana iya kamuwa da cutar daga cikin mamaci.

Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi a taron kamfanin dillancin labarai NAN a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel