Yanzu-yanzu: An gano mai coronavirus da ya tsere daga asibiti a Osun

Yanzu-yanzu: An gano mai coronavirus da ya tsere daga asibiti a Osun

Gwamnatin Jihar Osun ta gano mai dauke da kwayar cutar COVID-19 da aka ruwaito cewa ya tsere daga asibitin da aka killace su a jihar.

Ishmael Omipidan, babban sakataren watsa labarai na gwamnan jihar, ya ce an gano majiyancin a ranar Asabar da rana kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A cikin wani sako da Omipidan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya rubuta cewa, "An gano wanda ya bace mintuna kadan da suka gabata."

Yanzu-yanzu: An gano mai coronavirus da ya tsere daga asibiti a Osun
Yanzu-yanzu: An gano mai coronavirus da ya tsere daga asibiti a Osun
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

Wasu rahotanni sun ce mutane shida da suka kamu da cutar ta coronavirus ne suka tsere daga wurin da aka killace su.

Amma kwamishinan labarai na jihar, Funke Egbemode a baya ta ce an kirga mutanen da safe kuma an tabbatar da cewa mutum daya ne kawai ba a gan shi ba.

Kwamishinan ta kuma ce an tsaurara matakan tsaro a wurin da aka killace majinyatan. Mrs Egbemode ta bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta cigaba da aiki tukuru domin tabbatar da cutar ba ta yadu a jihar ba.

Cikin mutum 127 da suka dawo daga kasar Ivory Coast zuwa jihar ta Osun da aka killace, 22 cikinsu ne suka kamu da cutar ta coronavirus.

A cewar Cibiyar kare cutattuka masu yaduwa NCDC, cikin mutum 209 da aka tabbatar suna dauke da cutar, 20 daga cikinsu daga jihar Osun suka fito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel