Hanyoyin da Najeriya ke bi wajen hana yaduwar Coronavirus abin burgewa ne - Majalisar Dinkin Duniya

Hanyoyin da Najeriya ke bi wajen hana yaduwar Coronavirus abin burgewa ne - Majalisar Dinkin Duniya

- Majalisar dinkin duniya ta jinjinawa Najeriya a kan yadda ta dauka mataki a kan barkewar muguwar annobar coronavirus

- Sakataren majalisar, ya kwatanta Najeriya da kasa a nahiyar Afrika mai tasowa amma kuma mai kwazo

- Ya sabunta kiran shi ga kasashen duniya da ke fama da yaki irinsu Yemen, Syria da Libya da su yada makamai don a samu damar yakar annobar coronavirus

Majalisar dinkin duniya ta jinjinawa Najeriya a kan yadda take kokarin shawo kan annobar coronavirus.

A nahiyar Afrika, kasar Najeriya ce kasar da ta fi kowacce yawan mutane. Tana da mutane miliyan 200 amma mutane 210 ke dauke da muguwar cutar coronavirus. A hakan kuwa mutane biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar.

Hanyoyin da Najeriya ke bi wajen hana yaduwar Coronavirus abin burgewa ne - Majalisar Dinkin Duniya

Hanyoyin da Najeriya ke bi wajen hana yaduwar Coronavirus abin burgewa ne - Majalisar Dinkin Duniya
Source: Depositphotos

Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, yayin zantawa a kan ci gaban a New York, ya kwatanta Najeriya da kasa mai habaka wacce ta nuna matukar kokari wajen shawo kan barkewar annobar.

"Zan iya cewa wasu daga cikin kasashen nan masu tasowa sun nuna matukar kokari wajen martani a kan annobar.

"Na matukar jin dadin ganin hakan. A misali dai Najeriya ta yi kokari da gaggawar samar da asibiti. Na ga gazawa a kasashen da suka fi ta ci gaba don basu dauka matakin gaggawa ba."

KU KARANTA: Magidanci ya bayyana cewa iyalinsa duka sun kamu da Coronavirus ciki har da 'ya'yansa guda 11

Ya kara sabunta kiran shi ga kasashen da ke fama da yaki kamar su Syria, Libya da Yemen. Ya bukace su da su yada makamai tare da hada kai wajen yakar annobar da ta damu duniya.

"Akwai yuwuwar zuwan mummunan lamari," Guterres ya ce ga kasashen da ke fama da yaki.

"Guguwar annobar Coronavirus na zuwa duk inda ake yakin. Cutar ta nuna cewa za ta iya tsallaka iyakokin kasashe, ta tagayyara su sannan ta kwashe rayuka.

"Amma kuma akwai babbar tazara tsakanin cewa za a yi da kuma aikatawa. Banbanci ne babba tsakanin sasanci da kuma sadaukar da rayukan jama'a," Guterres yace.

"Da yawa daga cikin halin da muke ciki, ba a saduda ba kuma kullum fadan karuwa yake yi." Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel