Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Gwamna Ortom (Hotuna)

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Gwamna Ortom (Hotuna)

- Sakamakon gwajin kwayar cutar coronavirus da aka yi wa Gwamna Samuel Ortom ya nuna baya dauke da cutar

- Mataimakin gwamnan Injiniya Benson Abounu da Kwamishinan kudi na jihar, David Olofu su ma ba su kamu da cutar ba

- Gwamnan ya jadadda wa mutanen jihar cewa gwamnatinsa za ta cigaba da daukan matakan ganin cewa cutar ba ta yadu a jihar ba

Gwamna Samuel na jihar Benue da mataimakinsa Injiniya Benson Abounu da kwamishinan Kudi da Tattalin Arziki, David Olofu duk ba su kamu da cutar coronavirus ba kamar yadda sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna.

Daily Trust ta ruwaito cewa a safiyar ranar Alhamis ne Ortom ya yi gwajin na coronavirus domin sanin matsayinsa.

Mai magana da yawun gwamnan, Terver Akase, cikin wata sanarwar ta ya fitar a safiyar ranar Asabar ya bayyana cewa mai gidansa ya na karfafawa mutanen Benue su tafi su yi gwakin na COVID-19.

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Gwamna Ortom

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Gwamna Ortom
Source: UGC

DUBA WANNAN: Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

Ortom, a cikin sanarwar, ya yabbawa kwamitin kar ta kwana na jihar kan yaki da yaduwar cutar ta coronavirus da dukkan mutane da kungiyoyi da suke bayar da gudunmawarsu domin ganin an kawo karshen wannan annobar.

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Gwamna Ortom

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Gwamna Ortom
Source: UGC

Ya bayyana jin dadinsa ganin cewa baya ga mutum na farko da aka samu da cutar a jihar, dukkan wadanda aka yi wa gwajin a baya ba su dauke da kwayar cutar.

Gwamnan ya bukaci mutanen jihar su cigaba da yin tsafta da wanke hannuwansu da sabulu da ruwa da kuma man kashe kwayoyin cuta wato sanitizer da kuma takaita cudanya domin gudun kamuwa daga cutar.

Ya tabbatar wa mutanen jihar cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin ganin cewa cutar ba ya yadu tsakanin mutane a jihar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel