Jerin masu kudi 9 na duniya da arzikinsu yake karuwa a wannan lokaci na Coronavirus

Jerin masu kudi 9 na duniya da arzikinsu yake karuwa a wannan lokaci na Coronavirus

- Sakamakon barkewar muguwar annobar coronavirus, kasuwanci da yawa a duniya sun tarwatse

- 'Yan kasuwa na ta koke da korafin faduwar da suka yi sakamakon annobar coronavirus

- Wasu 'yan kasuwa na duniya kuwa sun sauya akalar kasuwancinsu ne zuwa abubuwan da ake bukata a halin yanzu

Kanun labarai na kwanakin nan na bayyana faduwar da 'yan kasuwa suke yi ne sakamakon muguwar annobar coronavirus.

Akwai kuwa jama'ar da ke ta kokarin taimakon masu karamin karfi balle a irin wannan lokacin. Wannan ya hada da sadaukan kowacce rana da suka hada da likitoci da malaman jinya wadanda suka sadaukar da rayukansu don majinyata.

Akwai masu siyar da kayan abinci da kuma magunguna tare da iyaye masu wayar da kan yara.

Amma kuma duk da hakan, akwai manyan 'yan kasuwan da arzikinsu ke habaka duk da cewa suna taimakon jama'a a fadin duniya.

Ga 'yan kasuwan kamar haka:

1. James Dyson

Kamfanin dan kasuwar suna samar da na'urorin taimakon numfashi ne a halin yanzu. Za su samar da har 15,000 wanda gwamnatin Birtaniya za ta siya. Na'urar dai ana amfani da ita ne a fadin duniya don taimakon jama'a masu dauke da muguwar cutar numfashi.

2. Jack Ma

Shine wanda yafi kowa arziki a kasar China kuma mamallakin Alibaba. A yayin da kasar Rasha ta ba China takunkumin fuska na sama da dala miliyan daya, ya ba Rasha din kayan gwajin cutar har 200,000.

3. Elon Musk

Tesla ya mayar da ayyukan kamfanonin shi ne a tsakiyar watan Maris din da ta gabata wajen samar da na'urorin taimakon numfashi.

4. Steve & Connie Ballmer

Tsohon mamallakin Microsoft ne. A tare da matar shi ne suka bada gudumawar dala miliyan 25 don farfado da tattalin arzikin Los Angeles wanda ya durkushe sakamakon annobar.

5. Marc Benioff

A shafin shi na twitter ne Benioff ya bayyana wasu matakai na shawo kan cutar. Za a samar da na'urorin taimakon numfashi, assasa samar da magunguna da kuma rigakafi, sai kuwa gaggauta gwaji.

Washegari kuwa ya bayyana cewa kamfanin shi zai fara wadannan ayyukan.

6. Bill Gates

Ta gidauniyar shi ne ya bada gudumawar dala miliyan 50 don tallafi wajen samar da maganin muguwar cutar tare da hana yaduwarta. Ya mika talkafin ne ga kamfanonin hada magunguna 12.

7. Mark Zuckerberg & Priscilla Chen

Mamallakin Facebook din ya bada gudumawar dala miliyan 25 don assasa samar da rigakafi da maganin muguwar cutar. Hakazalika, ya samar da hanyar tallafawa masu kananan kasuwanci a Facebook.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng