Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

Shugaban kungiyar musulunci ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah, JIBWIS, a jihar Plateau, Sheikh Sani Jingir, daga karshe ya yi biyaya ga dokar Gwamna Simon Lalong na hana duk wata taro na sama da mutane 50 a jihar domin kare yaduwar cutar coronavirus.

Idan ba a manta ba, Sheikh Jingir ya yi wa daruruwan mutane limancin sallar Juma'a a masallacinsa na 'Yantaya a makon da ta gabata a ranar 27 ga watan Maris duk da dokar da gwamnatin jihar ta saka.

Daga bisani, hukumar 'yan sandan farar kayan SSS sun gayyace shi ofishinsu game da saba dokar da ya yi na gwamnatin jihar a wannan lokacin da ake kokarin dakile yaduwar cutar.

Covid-19: Sheikh Jingir ya bi umurnin Lalong, ya yi sallar Juma'a a gida
Covid-19: Sheikh Jingir ya bi umurnin Lalong, ya yi sallar Juma'a a gida
Asali: Facebook

Covid-19: Sheikh Jingir ya bi umurnin Lalong, ya yi sallar Juma'a a gida
Covid-19: Sheikh Jingir ya bi umurnin Lalong, ya yi sallar Juma'a a gida
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An rufe masallacin da matasa suka yi wa jami'an yaki da coronavirus rajamu (Hotuna)

Yayin amsa tambayoyin a ofishin DSS, an ruwaito cewa an tilastawa Sheikh Jingir rubuta takardar rantsuwa ta jadadada mubaya'arsa ga gwamnatin jihar.

Covid-19: Sheikh Jingir ya bi umurnin Lalong, ya yi sallar Juma'a a gida
Covid-19: Sheikh Jingir ya bi umurnin Lalong, ya yi sallar Juma'a a gida
Asali: Facebook

A yau Juma'a, Daily Nigerian ta ruwaito cewa ba a ga Sheikh Jingir ba a harabar masallacin a lokacin sallar Juma'a inda wasu masallata da suka yi sallar su a masallacin na 'Yantaya.

Wata majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa ya yi sallarsa ne a masallacin gidansa tare da mutane kalilan kamar yadda hotunan ke nuna wa.

A baya-bayan nan dai Sheikh Jingir ya janyo cece-kuce tsakanin mutane saboda kin biyaya ga dokar gwamnatin da kuma ikirarin da ya ke yi na cewa bai amince akwai cutar coronavirus ba.

An ruwaito cewa Sheikh Jingir ya yi ikirarin cewa bullar annobar ta coronavirus ba komai bane illa sharri da makirci na Yahudawa da ke kokarin dakile musulunci da musulmi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel