Tashin hankali: An fara gina makabarta mai girman filin kwallo guda biyu a kasar Ingila saboda mutuwar da mutane suke kan Coronavirus

Tashin hankali: An fara gina makabarta mai girman filin kwallo guda biyu a kasar Ingila saboda mutuwar da mutane suke kan Coronavirus

- Gwamnatin Ingila ta fara gina katafariyar ma'adanar gawawwaki wacce ta yi girman filin kwallo biyu

- Kamar yadda wasikar sanar da mazauna yankin ta bayyana, 'yan uwan mamatan ba za su samu ziyartarsu ba saboda dokokin masana kiwon lafiya

- Gwamnatin tana gina katafariyar ma'adanar gawawwaki ne saboda akwai tsammanin yawan mamata daga cutar coronavirus za su hauhawa

Gwamnatin Ingila ta fara gina ma'adanar gawawwaki wacce ta kai girman filayen kwallo biyu a kusa da asibitin London. Gwamnatin ta yi hakan ne sakamakon yarda da tayi cewa za a ci gaba da mutuwa sakamakon cutar coronavirus, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya bayyana.

Ma'adanar gawawwakin ta wucin-gadin na nan a Wanstead Flats da ke gabas da birnin London, kusa da makarbarta.

Tashin hankali: An fara gina makabarta mai girman filin kwallo guda biyu a kasar Ingila saboda mutuwar da mutane suke kan Coronavirus
Tashin hankali: An fara gina makabarta mai girman filin kwallo guda biyu a kasar Ingila saboda mutuwar da mutane suke kan Coronavirus
Asali: Facebook

Majinyatan da suka mutu a sabon asibitin mai gadaje 4,000 ne za a adana a ma'adanar gawawwakin.

An sanar da mazauna kusa da wajen a kan ci gaban, lokacin da wasikar shugabar Newham, Rokhsana Fiaz ta isa musu.

KU KARANTA: Tirkashi: An kori dan majalisar wakilai daga jam'iyyar APC bayan ya zagi Sanata Danjuma Goje

Ta rubuta: "Wajen zai kasance ma'adanar gawawwaki kafin a birne su."

"Mun san cewa muguwar cutar coronavirus ta lamushe rayuka masu tarin yawa a Ingila. Mun san cewa yawan mamatan za su karu. Wannan shine martanin gwamnati a kan hakan."

Tashin hankali: An fara gina makabarta mai girman filin kwallo guda biyu a kasar Ingila saboda mutuwar da mutane suke kan Coronavirus
Tashin hankali: An fara gina makabarta mai girman filin kwallo guda biyu a kasar Ingila saboda mutuwar da mutane suke kan Coronavirus
Asali: Facebook

Kamar yadda wasikar ta bayyana, 'yan uwan mamatan ba za su iya ziyartar wurin ba saboda dokar masana kiwon lafiya.

Ingila dai ta tabbatar da cewa mutane 29,865 ne suka kamu da cutar coronavirus inda mutane 2,352 suka rasa rayukansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng