Yanzu Yanzu: Kwanan nan zan fito, dan Atiku ya yi magana daga inda aka killace shi

Yanzu Yanzu: Kwanan nan zan fito, dan Atiku ya yi magana daga inda aka killace shi

Mohammed Atiku, dan tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda ya kamu da cutar coronavirus, ya nuna yakinin cewa kwanan nan za a sallame shi.

Mohammed ya yi magana ne daga inda aka killace shi a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, a cikin wani bidiyo da mahaifinsa ya wallafa a shafin Twitter.

Ya ce: “A ranar 20 ga watan Maris, na kamu da cutar COVID-19 sannan aka kai ni cibiyar killace mutanen da suka kamu a asibitin koyarwa na jami’ar Gwagwalada inda na ci gaba da kasance a chan tun lokacin.

“A yanzu ina cikin kwana na 12 a nan kuma ina fatan zan fito kwanan nan-idan aka sake mun gwaji na gaba sannan sakamako ya yi kyau. Zan fito, ina da yakinin haka.

“Na yanke shawarar yin wannan bidiyo ne domin na yi magana kan halin da na ke ciki domin taimaka wa yan Najeriya.

“A ranakun farko ban nuna alamu ba sannan ina ta juyayi; na dan shiga tashin hankali da raunin zuciya, musamman kasancewa na farko a Abuja. Wannan shine babban kalubalen.

“Amma a kullun, ina kara samun karfin gwiwa, godiya ga tarin addu’o’i da fatan alkhairi da na dunga samu daga yan Najeriya da dama wadanda ban sani ba. Iyalaina da abokai da mutane da dama.

“Na gode Allah ina cikin koshin lafiya.”

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: 'Yar shugaba Buhari ta kammala killace kanta lafiya

Ga cikakken bidiyon a kasa:

Yayinda ya ke godiya ga ma’aikatan lafiya, ya bukaci yan Najeriya da su yi masu addu’ar kada wani cikinsu ya kamu yayinda suke kula da wadanda suka kamu.

Mohammed ya kuma shawarci yan Najeriya da su hada kai sannan su yaki cutar.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari na samun sauki sosai amma likitocinsa sun nemi ya kara hutawa sosai kamar yadda wasu majiyoyi na kusa dashi suka bayyana, jaridar The Cable ta ruwaito.

Na hannun damar Shugaban kasar ya kamu da cutar Coronavirus a makon da ya gabata amma ya fuskanci alamun ciwon kadan-kadan ne, in ji majiyoyi daga gidansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel