'Yan Najeriya za su yi tutsu idan aka tilasta su zaman gida babu abinci, babu haske - ASUU ta gargadi FG

'Yan Najeriya za su yi tutsu idan aka tilasta su zaman gida babu abinci, babu haske - ASUU ta gargadi FG

Kungiyar malamai masu koyarwa a jami'a (ASUU) a ranar Alhamis ta shawarci gwamnatin tarayya da na jihohi da su goyi bayan rufe kasar nan ta hanyar samar da kayayyakin bukata ga talakawa.

Kungiyar ta tabbatar da cewa sai an samar da bukatun jama'a ne sannan talakawa za su iya jurewa, ba tare da sun yi wa gwamnati bore ba.

ASUU ta ce har sai an samar da bukatun talakawa ne za a iya cimma manufar killace mutane da nesanta su da juna da hanasu haduwa a wurin taruka.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, a takardar da ya fitar, a kan annobar coviid-19, wacce ya ba manema labarai, ya ce dole ne a samar da isasshiyar wutar lantarki, ruwa da kuma abinci ba yankewa.

Ogunyemi ya bayyana cewa kungiyar za ta taimaka ta hanyar raba sinadarin tsaftace hannaye da kuma sauran kayayyakin da ake bukata don gujewa yaduwar muguwar cutar coronavirus.

An kuwa fara rabon ne a jami'ar Ibadan da jami'ar jihar Jos.

'Yan Najeriya za su yi tutsu idan aka tilasta su zaman gida babu abinci, babu haske - ASUU ta gargadi FG
Taron ASUU da Buhari
Asali: Facebook

Ya kara da cewa ASUU za ta ci gaba da iyakar kokarinta a fadin kasar nan.

Shugaban ASUU din ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi a kan su tabbatar da ba wa ilimi da kiwon lafiya fifiko bayan wannan annobar, tare da tabbatar da cewa za a hada kai wajen yakar cutar.

DUBA WANNAN: An gano ta barauniyar hanyar da masu cutar coronavirus 9 suka shigo Najeriya

"Samar da wutar lantarki, ruwan sha da kuma abinci tare da sauran bukatu shine mataki na farko da ya kamata a fara samarwa kafin samar da dokar da hana walwala. Har sai an cika wa jama'a bukatarsu ne sannan bukatar gwamnati za ta cika a kowanne mataki." Ya ce.

"Za mu iya cewa babu wata matsala da ta hada kan jama'a a karnika da yawa da suka shude kamar coronavirus. An koyi darussan da duniya bata taba koya ba. An gane kuskure a bangarorin kiwon lafiya da na shugabanci. Duniya na bukatar cibiyoyin lafiya. Za mu iya shawo kan tsoron wannan annobar ne idan duniya ta hada kai. ASUU za ta taimaka wajen yaki da hana yaduwar cutar nan," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng