Annobar Coronavirus: Sakamakon gwajin da aka yi ma wani mutumin Zaria ya fito

Annobar Coronavirus: Sakamakon gwajin da aka yi ma wani mutumin Zaria ya fito

Hukuma ta sako wani mazaunin garin Zaria na jahar Kaduna da ya dawo daga jahar Legas a ranar Juma’a, amma aka killace shi a babban asibitin Gambo Sawaba sakamakon zargin da ake yi na cewa yana dauke da kwayar cutar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito hukumar asibitin ta sallami mutumin ne bayan samun sakamakon gwajin da hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC, ta yi masa, wanda ya nuna tabbas mutumin ba ya dauke da cutar.

KU KARANTA: Boko Haram: Kasashen Najeriya, Nijar da Chadi sun kaddamar da sabbin hare hare

Mutumin mai suna Iliyasu Mukhtar ya koma Zaria ne daga jahar Legas, sai dai koda ya isa gida sai suka same shi yana fama da zazzabi, kuma baya iya numfashi yadda ya kamata, nan da nan aka garzaya da shi Gambo Sawaba don samun kulawa, inda a can aka killace shi don gudanar da bincike.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mukhtar ya yi wannan dogon tafiya ne a cikin wata budaddiyar motar daukan kaya. Amma babban likitan asibitin, Dakta Hussaina Adamu ta bayyana cewa a garin Kaduna aka yi ma Mukhtar gwajin.

“Sakamakon da ya fito ya nuna baya dauke da cutar, don haka yana fama ne da rashin lafiya da ta shafi shakar numfashi, kuma tuni ya fara samun sauki, saboda haka muka sallame shi. Amma ya kamata jama’a su cigaba da bin tsare tsare kare kai daga kamuwa da cutar.” Inji ta.

Daga karshe Dakta Hussaina ta yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani da suke zargi yana dauke da cutar ga asibiti ko wata cibiyar lafiya mafi kusa da su.

A wani labarin kuma, shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede ya bayyana cewa kamuwa da yayi da cutar Coronavirus ta sa ya zamto mutum mai tawali’u, tare da kaskantara da kan sa.

Punch ta ruwaito Babandede ya bayyana haka ne daga inda aka killace shi a karo ba farko, inda yace sakamakon gwajin da aka masa ne ya nuna yana dauke da cutar bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya a ranar 22 ga watan Maris.

Babandede ya nemi yan Najeriya su cigaba da addu’ar Allah Ya kiyaye yaduwar cutar, domin kuwa idan hakan ya faru zata kwashi rayukan jama’a da dama, kwanturolan ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo, inda yace jama’an kauyensu da sauran yan Najeriya suna ta masa addua’r samun sauki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel