Boko Haram: Kasashen Najeriya, Nijar da Chadi sun kaddamar da sabbin hare hare

Boko Haram: Kasashen Najeriya, Nijar da Chadi sun kaddamar da sabbin hare hare

Dakarun rundunonin Sojin kasashen Najeriya, Nijar da Chadi sun kaddamar da wasu sabbin hare hare domin bankado mayakan Boko Haram tare da fatattakarsu daga sabuwar mabuyar da suka koma na tsibirin Tunbuns dake tafkin Chadi.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa yan ta’addan sun tsere zuwa tsibirin sakamakon rakiyan Kura da Sojojin Najeriya suka musu daga inda suka saba kaddamar da hare hare a kan fararen hula mazauna kauyukan yankin.

KU KARANTA: Annobar Corona: Ku kama duk wanda kuka ga bai sa kyallen rufe fuska ba – Gwamna ga Yansanda

Daraktan sashin watsa labaru na shelkwatar Sojin Najeriya, Birgediya Benard Onyeuko ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar inda yace rundunar Soji ta kawance da ta hada da sashi na 2, kasar Chadi, sashi na 3, kasar Najeriya da sashi na 4, kasar Nijar.

“Rundunar kawancen ne ta kaddamar da wadannan sabbin hare hare domin fatattakar yan ta’addan daga tsibirin Tunbuns dake tafkin Chadi, da kuma lalata duk wani sansanin Boko Haram ko na ISWAP dake yankin.

“Idan za’a tuna biyo bayan shan wahala a hannun dakarun Sojin Najeriya ne yan Boko Haram suka tsere zuwa tsibirin inda daga can suke shirya hare harensu, wannan ne yasa rundunar kasashe masu kawancen Soji suka kaddamar da samamen domin gamawa da su.” Inji shi.

A wani labarin kuma, zaratan dakarun rundunar Sojin Najeriya dake aikin Operation Lafiya Dole sun samu nasarar halaka wani babban kwamandan kungiyar ta’addanci na Boko Haram, Abu Usamah tare da gomman mayakan ta’addanci.

Shugaban sashin watsa labaru na rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, inda yace Sojojin sun samu wannan nasara ne a karan battan da suka yi da Boko Haram a Gorgi, karamar hukumar Damboa.

A cewar Onyeuko, wannan nasara da rundunar Sojin Najeriya ta samu ya samar da wata babbar gibi a shugabancin kungiyar Boko Haram, ya kara cewa sun kwato bindigar AK-47 guda 2, albruusai, bindigar harba Bom da sauran ababe da dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel