Wata sabuwa: Tabin hankali na daya daga cikin sabuwar alamar kamuwa da Coronavirus

Wata sabuwa: Tabin hankali na daya daga cikin sabuwar alamar kamuwa da Coronavirus

- Likitoci a fadin duniya sun gano cewa cutar coronavirus ba huhu kadai take tabawa ba, har da kwakwalwa

- Idan zamu tuna, an bayyana sabbin alamun cutar wanda ya hada da rashin tantance wari ko kamshi

- Majinyata sakamakon cutar suna bayyana da matsanancin ciwon kai wanda ke iya taba sashin tunani da ke cikin kwakwalwarsu

Likitocin kwakwalwa na duniya sun ce kadan daga cikin wadanda suka kamu da muguwar cutar a kasashe masu tasowa na samun tabin kwakwalwa.

Duk da zazzabi, tari da kuma wahala wajen numfashi suna daga cikin alamomin kamuwa da cutar coronavirus, wasu majinyatan sun nuna wasu alamu na tabuwar kwakwalwa. Wadannan alamun sun hada da rashin tantance wari ko kamshi tare da ciwo na zuciya.

A farkon watan Maris, wani mutum mai shekaru 74 an shigar dashi dakin taimakon gaggawa a Boca Raton bayan yana fama da tari da kuma zazzabi. Bincike ya nuna yana fama da cutar lamoniya.

Bayan kwanaki kadan yayin da zazzabin shi yake karuwa, 'yan uwanshi sun mayar dashi asibiti. Yana numfashi da kyar amma ba ya iya ko fadin sunanshi. Baya iya magana ko kadan.

Majinyacin wanda aka gano yana da ciwo mai tsanani a huhun shi, baya iya ko matsar da hannuwanshi kuma yana suma. Likitoci sun zargi cewa yana fama da cutar coronavirus kuma daga baya hasashensu ya tabbata.

KU KARANTA: Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari

Likitoci a Detroit sun bayyana labarin wata mata da ke aiki da kamfanin jirgin sama amma shekarunta sun zarta 50. An gano tana dauke da cutar coronavirus ne bayan ta fara samu dimuwa kuma tana fama da ciwon kai. Abu kadan game da ciwonta take iya yi wa likitoci bayani. Tana samun kumburi a bangarori daban-daban na jikinta wanda daga baya hakan ya zama sanadiyyar mutuwarta.

Likitocin kwakwalwa a Wuhan, China, inda aka fara samun barkewar cutar ne suka fara bayyana alamomin cutar a yanar gizo.

Tun bayan wannan rahoton nasu, kwararru a kasashen Jamus, Faransa, Austria, Italiya da Holland tare da Amurka sun dinga lura da irin hakan a tattare da majinyata.

Wasu likitocin sun bayyana yadda ake kawo musu marasa lafiya da alamun tabuwar kwakwalwa amma daga bisani sai dai a tsincesu da cutar coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel