Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari

Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari

- A ranar Litinin da ta gabata ne gwamnatin jihar Zamfara ta ceto wasu mutane 57 daga gidan horo a Gusau, babban birnin jihar

- Kamar yadda bayani ya nuna, Gwamna Matawalle ya samu bayanan sirri a kan wanzuwar gidan inda ya tura kwamishinan ayyuka na musamman

- Kamar yadda malamin ya bayyana, ba su duka amma suna horarwa ta yadda mutum zai koma halayya ta gari cikin watanni uku zuwa shida

A ranar Litinin da ta gabata ne gwamnatin jihar Zamfara ta bankado wata cibiyar horo da ke Gusau, babban birnin jihar. An samu ceto mutane 57 wadanda aka daure da kaca.

An gano cewa Gwamna Matawalle ne ya samu bayanan sirri a kan wanzuwar cibiyar kuma da gaggawa ya sanar da kwamishinan ayyuka na musamman wanda ya jagoranci kungiyar da ta hada da jami'an tsaro da kuma jami'ai daga ma'aikatar mata don zuwa wurin.

Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Asali: Facebook

Bayan isarsu cibiyar, a kalla mata da maza 57 aka samu a gidan wanda wani Malam Iliyasu Abdullahi Gamagiwa ke shugabanta. An samu jama'ar gidan daddaure da kaca.

Da gaggawa jami'an tsaron suka saki jama'ar tare da kwashesu inda aka ciyar da su kafin daukar mataki na gaba.

Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Coronavirus ce babbar masifar da ta sami duniya tun bayan yakin duniya na biyu - Majalisar Dinkin Duniya

Kwamishinan ya ce an ajiye wadanda ake horarwar a mummunan hali ba tare da ana ciyar da su yadda ya dace ba. Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta fitar da bayanan mutanen don gano shekarun su tare da 'yan uwansu.

A yayin zantawa da manema labarai kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, Malam Abdullahi Iliyasu ya ce gidan horarwar ya kai shekaru 30 da kafuwa.

Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Asali: Facebook

Ya ce yana karbar N15,700 don rijista sai kuma N10,000 duk wata don ciyarwa da magani.

"Ana daure mutum na watanni a kalla uku zuwa shida kafin a mayarwa iyayenshi. Amma kuma bamu azabtar da jama'a. Muna da saita musu halinsu ne kuma su koma mutane na gari," ya ce.

Amma kuma wasu daga cikin wadanda aka ceto din sun ce sau daya ake basu abinci a rana. Kuma idan aka kawo mutum a karon farko, ana iya yi mishi bulala 50 a take. Ana zuba su ne a daki daya ba tare da an bar iska mai tsafta na iso musu ba.

Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Asali: Facebook

Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Hotuna: Yadda gwamnatin Zamfara ta ceto wasu bayin Allah 57 daure cikin ankwa a wani gidan mari
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel