Coronavirus ce babbar masifar da ta sami duniya tun bayan yakin duniya na biyu - Majalisar Dinkin Duniya

Coronavirus ce babbar masifar da ta sami duniya tun bayan yakin duniya na biyu - Majalisar Dinkin Duniya

- Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa cutar coronavirus ce babban kalubalen da duniya ta kara fuskanta bayan yakin duniya na biyu

- Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya bayyana tsananin damuwar shi a kan halin da cutar ta jefa kasashen duniya

- Ya ce akwai yuwuwar shawo kan matsalar amma idan aka manta da dukkan siyasa tare da hada kai

Majalisar dinkin duniya (UN) ta bayyana cutar coronavirus da mafi munin annobar da ta samu duniya bayan yakin duniya na biyu.

Wannan jan kunnen ya biyo bayan mutuwar da ake ta samu a kasar Amurka wacce ta zarce ta kasar China, inda aka fara samun cutar.

Coronavirus ce babbar masifar da ta sami duniya tun bayan yakin duniya na biyu - Majalisar Dinkin Duniya

Coronavirus ce babbar masifar da ta sami duniya tun bayan yakin duniya na biyu - Majalisar Dinkin Duniya
Source: UGC

Cutar dai ta kama mutane 860,000 a fadin duniya inda kasar Amurka ta rasa mutane 800 a ranar Talatar da ta gabata. Hakan ne yasa yawan mutanen da suka rasa suka kai 3,700.

Cutar ta lashe rayuka masu yawa a kasashen Spain, Ingila, Faransa da Italiya wadanda hakan ya matukar tada hankulan gwamnatocinsu.

Sauran nahiyoyin da suka hada da Afrika, Amurka ta Kudu da Australia duk suna fama da barkewar muguwar cutar. Hakazalika barkewar annobar ta kawo faduwa warwas na farashin danyen man fetur wanda haka ya kawo durkushewar tattalin arziki a duniya.

Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya nuna damuwar shi a kan yadda annobar ta kara assasa rashin jituwa tsakanin kasashen duniya.

KU KARANTA: Shugaban Colorado ya karyata wanzuwar cutar Coronavirus, ya bukaci wanda yake da ita ya tofa masa yawu a baki

Guterres ya ce rashin jituwar ya biyo bayan bullar cutar da ta zama babban kalubale ga kowacce kasa ta duniya. Za ta iya taka rawar gani kuwa wajen jefa kasashen duniya cikin durkushewar tattalin arzikin da ba a taba samun irin shi ba.

"Duba da dalilai biyu din nan tare da yuwuwar rashin daidaituwar da za su iya kawowa, za mu iya cewa wannan ne babban kalubalen da duniya take fuskanta bayan yakin duniya na biyu," ya sanar da manema labarai a ranar Talata.

"Za a iya samo mafita ne matukar an hada kai kuma mun manta da wata siyasa tare da fahimtar cewa jarabawace ta shafi kowa," Guterres ya kara da cewa.

Guterres ya bayyana cewa hatta kasashe masu karfin tattalin arziki sun jigata ballantana su taimakawa kasashe masu tasowa.

"Muna fuskantar alkibla a hankali amma akwai bukatar mu kara zage-damtse don yakar muguwar cutar nan." Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel