Lamari ya baci: Kasar Rasha ta fara aikawa da kasar Amurka kayan tallafi saboda cutar Coronavirus

Lamari ya baci: Kasar Rasha ta fara aikawa da kasar Amurka kayan tallafi saboda cutar Coronavirus

- A wani sabon salon nuna goyon baya ga kasashe biyu masu adawar neman rinjaye a duniya, kasar Rasha ta bayyana matsayarta

- Jirgin rundunar sojin kasar Rasha dankare da kayayyakin tallafi a kan yakar cutar coronavirus ne ya dumfari kasar Amurka

- Kamar yadda shugaban kasar Rasha din ya bayyana, shugaba Trump ya amince da karbar tallafin da kasarsa ta mika ga kasar Amurka din don yakar cutar coronavirus

A wani salon nuna goyon baya tsakanin 'yan adawa biyu da ke fatan zama mafiya rinjaye a duniya, kasar Rasha ta kaiwa kasar Amurka tallafin kayayyakin asibiti don yakar cutar coronavirus da ta addabi kasar. Muguwar cutar ta yi nasarar lashe rayuka 3,700 na 'yan kasar Amurka.

Lamari ya baci: Kasar Rasha ta fara aikawa da kasar Amurka kayan tallafi saboda cutar Coronavirus

Lamari ya baci: Kasar Rasha ta fara aikawa da kasar Amurka kayan tallafi saboda cutar Coronavirus
Source: UGC

Jirgin saman rundunar sojin Rasha din ya tashi ne a ranar Laraba 1 ga watan Afirilu inda ya nufi kasar Amurka dankare da na'urorin asibiti da takunkumin fuska na tallafi don taimakon kasar wajen yakar muguwar cutar coronavirus, gidan talabijin din kasar Rasha ya ruwaito.

KU KARANTA: Ku lallaba mazajenku kada ku tsokana rigimar da tafi ta Coronavirus - Budurwa ta shawarci matan aure

Shugaban kasa Vladimir Putin ya bayyana za su taimakawa kasar Amurka din ne ta tattaunawar wayar tafi da gidan ka tsakanin shi da shugaba Donald Trump a ranar Litinin. A tattaunawar ne suka zanta a kan babbar hanyar da za ta zama mafita wajen yakar cutar.

"Trump ya amince da taimakon da za mu kai musu," Kremlin mai magana da yawun Dmitry Peskov ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Interfax a daren Talata.

Hakazalika, ma'aikatar lamurran harkokin waje ta kasar Rasha ta wallafa a shafinta na twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel