Ku lallaba mazajenku kada ku tsokana rigimar da tafi ta Coronavirus - Budurwa ta shawarci matan aure
- Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ta shawarci mata a kan zama da mazansu a wannan lokacin hutun dolen
- Ta ce ba ta goyon bayan namiji ya daga hannu ya daki mace amma wasu matan halayyarsu ce ke ja musu
- Kalubalantar namiji kuwa babbar matsala ce don babu namijin da ke son kalubale balle daga matar shi
Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ta shawarci mata da su kiyaye kalamansu da sauran lamurransu a yayin da maza ke kulle a gida sakamakon annobar coronavirus. A cewarta, hakan ne kadai zai tseratar da mata daga shan duka a wurin mazansu.
Budurwar mai sun Mma Eka ta bayyana cewa bata goyon bayan namiji ya daga hannun shi a kan matarshi amma kuma kada matar da ta kai namijin makura. Kowanne namiji yana da iya abinda zai iya jurewa amma zai iya barna idan aka kure shi.
"Bana goyon bayan namiji ya daga hannu a kan matar shi komai kuwa laifin da tayi mishi a duniya. Amma kuma babu dadi mace ta kai namiji makura don kowanne namiji yana da iyakar hakurin shi.
KU KARANTA: An yankewa wani mutumi mai coronavirus hukuncin kisa a Saudiyya bayan ya tofa yawu a jikin kofa dan wani ya taba ya dauki cutar
"Ku daina yi wa maza amfani da kalamai irinsu: Ba za ka iya yin komai a kai ba, me za ka iya yi? Yi duk abinda za ka iya... Wadannan kalaman na kalubale ne kuma babu namijin da zai iya jure ana kalubalantar shi. A dena amfani da baki kamar lalataccen famfo." Ta ce.
Ta kara da bayyana yadda wasu matan ke kaiwa ga shake wuyan rigar namiji ko dukan kirjin shi tare da ihun cewa ko zai kashesu ba za su daina abinda suke yi ba.
"Kada ki bata mijinki da kanki don daga baya ke za ki yi dana-sani. Kun ga wannan hutun dole da suke yi a gida, kada ki yi ganganci idan baki son ganin aikin ganganci. A jiya na shawarci maza a kan yadda za su zauna lafiya da matansu a wannan lokacin, yanzu lokacin ki ne." Ta kara da cewa.
Kamar yadda tace, an san mata da kaifin harshe amma mace mai hankali ta san lokacin da za ta yi magana. Akwai karin magana mai cewa "Za ka iya dana-sani a kan kalamanka amma ba za ka iya taba dana-sanin shirunka ba."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng