Ku tsaftace kawunanku da muhallanku don yaki da Corona – Sarkin Kano ga Kanawa

Ku tsaftace kawunanku da muhallanku don yaki da Corona – Sarkin Kano ga Kanawa

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga jama’an jahar Kano su cigaba da bin dukkanin matakan kare kai daga kamuwa da annobar cutar Coronavirus, tare da yin biyayya ga shawarwarin masana kiwon lafiya.

Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito Sarkin ya bayyana haka ne yayin da yake yi ma al’ummar Kano jawabi a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, inda ya koka tare da bayyana damuwarsa kan yadda ake samun yawaitan cutar a Najeriya.

KU KARANTA: Annobar Corona: Ku kama duk wanda kuka ga bai sa kyallen rufe fuska ba – Gwamna ga Yansanda

Sarki ya ce ya umarci dukkanin hakimansa da dakatai da kuma shuwagabannin addinai su cigaba da sa ido a kan jama’a, kuma su kai rahoton duk inda aka samu wani dake dauke da alamomin cutar da basu gane bag a masana kiwon lafiya.

“Ina kira ga jama’a da su cigaba da dabbaka matakan kariya daga cutar Coronavirus kamar su tsaftar jiki, wankin hannu da sabulu da ruwa, kauce ma shiga cunkoson jama’a da kuma zama a gida kamar yadda masana kiwon lafiya suka tabbatar.

“Al’ada ce ta kakanninmu wayar da kawunan jama’ansu tare da ilimantar da su a kan yadda zasu kiyaye yaduwar cututtuka saboda aikinmu ne mu kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu.” Inji shi.

Haka zalika mai martaba Sarki ya yi kira ga gwamnatin jahar Kano ta bayar da tallafi ga gajiyayyu da marasa karfi domin taimaka ma wadanda wannan annoba ta shafa, sa’annan ya nemi yan Najeriya su dage da addu’a don ganin bayan annobar.

Daga karshe Sarkin ya yaba ma gwamnatin tarayya da gwamnatin jaha bisa kokarin da suke yi tare da kwararan matakai da suke dauke don dakile yaduwar cutar nan mai toshe numfashi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Cross Rivers, Farfesa Ben Ayade ya umar jami’an tsaron jahar da su tabbata sun kama duk wani mutumin da suka gan shi yana tafiya a kan titi ba tare da yana sanye da kyalle rufe fuska ba.

Ben ya ce yana so Yansanda su fara dabbaka wannan umarni ne daga ranar Juma’a, 3 ga watan Afrilu, duk kuwa da cewa hukumar kiwon lafiya ta Duniya, WHO, ta bayyana cewa marasa lafiya ne kadai suke bukatar amfani da kyallen, ko kuma masu jinyarsu.

Gwamnan ya kaddamar da wannan doka ne duk da cewa ba’a samu bullar cutar Coronavirus a jahar ba, amma ya ce ya dauki wannan mataki ne na dakile yaduwar cutar zuwa jaharsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng