Annobar COVID-19: Fadar Shugaban Najeriya ta lissafo jerin kokarin Buhari
Fadar shugaban kasa ta bakin Femi Adesina ta jero wasu matakai da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauko a Najeriya bayan barkewar cutar Coronavirus.
Ga ayyukan da shugaban kasar ya yi daga lokacin da cutar ta fara bayyana zuwa yanzu:
28 ga Junairu: Kafin shigowar cutar Najeriya, gwamnatin tarayya ta tsananta bincike a filayen tashi da saukar jirage a Najeriya da nufin gano masu cutar.
28 ga Junairu: Hukumar NCDC ta bada sanarwar da shirya wadanda za su shawo kan wannan annoba idan har cutar ta barke.
31 ga Junairu: gwamnatin tarayya ta kara shiri a daidai lokacin da WHO ta ce Najeriya ta na cikin wuraren da cutar za ta iya kamari.
27 ga Fubrairu: Ministan lafiyan Najeriya, Dr. Osagie Ehanire, ya sanar da cewa an samu wanda ya fara shigowa da wannan cuta.
9 ga Maris: Buhari ya kaddamar da kwamiti na musamman da zai yi yaki da yaduwar COVID-19.
17 ga Maris: Gwamnatin Najeriya ta dakatar da bikin wasannin da aka shirya za a ayi a Benin, jihar Edo.
18 ga Maris: Shugaban kasa Buhari ya hana wadanda su ka fito daga wasu kasashe 13 shigowa Najeriya.
18 ga Maris: Dakatar da horaswar da ake yi wa masu yi wa kasa hidima a sansanin NYSC a fadin Najeriya.
18 ga Maris: Hukumar NFF da tsaida duk wasu wasannin kwallon kafa na makonni hudu.
18 ga Maris: Diyar shugaban kasa ta killace kanta bayan dawowa daga Ingila.
20 ga Maris: Gwamnatin Najeriya ta rufe Makarantun Sakandare da na gaba da Sakandare.
20 ga Maris: An shigar da wasu kasashen cikin sahun wadanda aka hana shigowa Najeriya.
20 ga Maris: Gwamnati ta rufe filayen sauka da tashin jiragen saman Enugu, Fatakwal da Kano.
21 ga Maris: Hukumar NRC ta dakatar da aikin jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna.
KU KARANTA: COVID-19: Buhari zai taimakawa mutum miliyan 11 a Najeriya

Asali: UGC
21 ga Maris: Najeriya ta rufe sauran filayen sauka da tashin jiragen Abuja da Legas.
23 ga Maris: CJN, Tanko Muhammad, ya bada umarnin a rufe kotu a Ranar 24 ga Watan Maris.
23 ga Maris: Buhari ya amince da dakatar da taron FEC da NCS a Najeriya.
23 ga Maris: Hukumar zabe na kasa INEC ta tsaida duk wasu aikinta.
24 ga Maris: Hukumar JAMB ta tsaida ayyukanta cak na tsawon makonni biyu.
24 ga Maris: Hukumar NECO ta fasa gudanar da jarrabawar shiga Makarantun Sakandaren gwamnati a fadin Najeriya.
24 ga Maris: Hukumar FCTA ta bada umarnin a rufe shaguna da kasuwanni.
24 ga Maris: Haramta sallah da zuwa coci a birnin tarayya Abuja.
25 ga Maris: An garkame filin sauka da tashin jiragen sama da ke Asaba, Delta.
27 ga Maris: An rufe iyakokin kasan Najeriya.
26 ga Maris: CBN ta bada sanarwar gudumuwar da aka fara badawa domin yaki da cutar COVID-19.
26 ga Maris: Gwamnatin tarayya ta karbi kayan tallafi daga kasar Sin.
27 ga Maris: Gwamnatin tarayya ta ba Legas Naira biliyan 10 domin yaki da annobar COVID-19.
27 ga Maris: Gwamnatin Buhari ta yabawa matakan da CBN ta dauka. An fara shirin sake duba kasafin kudin 2020.
27 ga Maris: Buhari ya bukaci Ma’aikatar kasuwanci da kungiyar MAN su fara hada magunguna da kayan abinci.
27 ga Maris: Ofishin HCSF ya fitar da jawabi, ya na umartar ma’aikata su daina zuwa ofis.
29 ga Maris: Shugaban kasa Buhari ya yi wa ‘Yan kasa jawabi a karon farko.
29 ga Maris: Shugaban kasa ya sa hannu a dokar COVID-19 na shekarar 2020.
30 ga Maris: Dokar hana fita da shugaban kasa ya sa ta fara aiki a Legas da Abuja da kwaye.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng