Sakon faifan bidiyon masu dauke da covid-19 ga sauran 'yan Najeriya

Sakon faifan bidiyon masu dauke da covid-19 ga sauran 'yan Najeriya

- Wasu daga cikin masu dauke da kwayar cutar covid-19 da aka killace a jihar Legas sun aiko muhimman sako a faifan bidiyo zuwa ga sauran 'yan Najeria

- Marasa lafiyar sun shawarci 'yan Najeriya su zauna a gida, tare da yi musu gargadin cewa cutar coronavirus gaskiya ce

- Kazalika, masu dauke da cutar sun mika godiya ga ma'aikatan lafiya da ke dawainiya da su tare da basu kulawa

Wasu daga cikin wadanda sakamakon gwaji ya tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19, kuma aka killcesu a asibitin cututtuka masu yaduwa (IDH) da ke Yaba a jihar Legas, sun aiko sako a ciki faifan bidiyo domin fadakar wa tare da wayar da kan sauran 'yan Najeriya a kan kwayar cutar.

Kazalika, masu dauke da kwayar cutar sun mika godiyarsu ga ma'aikatan lafiya, musamman likitoci da mataimakunsu, bisa dawainiyar da suke yi da su a yayin da suke a killace.

Bidiyon masu dauke da kwayar cutar, wanda gwamnan jihar Legas, Babjide Sanwo-Olu, ya fara wallafa wa a shafinsa na tuwita, ya cigaba da zagayawa a dandalin sada zumunta a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2020.

A cikin faifan bidiyon, an ga masu dauke da kwayar cutar su 12 dauke da rubutattun sakonni na wayar da kan jama'a a jikin takarda suna rike da shi.

Dukkansu sun yi shigar kayan kariya da takuntumin rufe baki, lamarin da yasa ba za a iya gane wadanda suka bayyana a jikin bidiyon ba.

DUBA WANNAN: Ramuwar gayya: Shekau ya saki sabon sako bayan sojojin kasar Chadi sun kashe masa dumbin mayaka

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, wata karamar yarinya, mai shekaru 8 kacal a duniya, ta bayar da gudunmawar kudin domin a yaki cutar covid-19 a Najeriya.

Karamar yarinyar, Vera Akpan, 'yar asalin jihar Delta, ta fasa bankinta na ajiyar kudi tare da rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, Muhamnadu Buhari, domin tambayarsa a kan yadda za ta bayar da dukkan kudin ga gwamnatin tarayya.

Ta bayyana cewa ta zabi bayar da kudin ne saboda bukatar kudade da gwamnati ke yi domin shawo kan annobar cutar COVID-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng