An yankewa wani mutumi mai coronavirus hukuncin kisa a Saudiyya bayan ya tofa yawu a jikin kofa dan wani ya taba ya dauki cutar

An yankewa wani mutumi mai coronavirus hukuncin kisa a Saudiyya bayan ya tofa yawu a jikin kofa dan wani ya taba ya dauki cutar

- Hukumomi a kasar Saudi Arabia sun damke wani mutum da ake zargi da yada cutar coronavirus

- An ga mutumin yana tofa miyau a kan kwandon siyayya da kuma kofofin wani kanti bayan an tabbatar yana da cutar

- Kamar yadda hukumomi suka bayyana, akwai yuwuwar mutumin ya fuskanci hukunci wanda zai iya kaiwa da na kisa saboda an tabbatar da cewa yana dauke da cutar

Hukumomi a kasar Saudi Arabia sun damke wani mutum da ke tofa miyau a kan kwandon siyayya da kofofi bayan an gano yana dauke da cutar coronavirus.

Lamarin ya faru ne a wani kanti da ke Arewacin kasar. Tuni kuwa aka damke wanda ake zargin bayan ma'aikatan kantin sun gano shi.

A yayin da yake tsare, mutumin wanda ba asalin dan kasar bane ya bayyana cewa yana dauke da muguwar cutar coronavirus. Yana rayuwa ne a birnin Baljurashi da ke yankin kudu maso yammacin Al Bahah. Ya kuwa yi wannan ta'asar ne duk da ya san yana dauke da muguwar cutar.

Bayan an tabbatar yana dauke da cutar, hukumomi sun bukaci dukkan wadanda suka shiga kantin da su garzaya don gwaji. A halin yanzu kuwa suna ta kokarin ganowa ko wanda ake zargin ya yada kwayar cutar a wasu wuraren na daban.

KU KARANTA: Kasashen da muke kallo a matsayin wadanda za su taimaka mana suma neman taimakon suke yanzu - Gwamnatin tarayya

Hukumomi a kasar Saudi Arabia din sun yanke shawarar cewa za a hukunta wanda ake zargin har ya kai ga kashe shi. Saboda a bayyane yake ya san da kwayar cutar a jikinshi kuma da burin halaka jama'a yake hakan.

A ranar 27 ga watan Maris, Saudi Arabia na da mutane 1,012 da aka tabbatar suna dauke da cutar coronavirus da kuma mutane uku da suka mutu, kamar yadda jami'ar John Hopkins ta bayyana.

Kasar Saudi Arabia ta dau matakan hana yaduwar cutar, wadanda suka hada da dakatar da saukar jiragen sama na wasu kasashen tare da dakatar da Umrah. Kasar ta kara da rufe masallatai, makarantu, kantina da wuraren cin abinci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel