Covid-19: Wata yarinya mai shekaru 8 ta rubutawa Buhari wasika, ta bayar da tallafin N2,350

Covid-19: Wata yarinya mai shekaru 8 ta rubutawa Buhari wasika, ta bayar da tallafin N2,350

A yayinda attajirai da sauran masu sukuni ke cigaba da bayar da gudnunmawarsu ga gwamnati a matakin jiha da na tarayya, wata karamar yarinya ta bayar da gudunmawarta.

Karamar yarinyar, Vera Akpan, 'yar asalin jihar Delta, ta fasa bankinta na ajiyar kudi tare da rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, Muhamnadu Buhari, domin tambayarsa a kan yadda za ta bayar da dukkan kudin ga gwamnatin tarayya.

Ta bayyana cewa ta zabi bayar da kudin ne saboda bukatar kudade da gwamnati ke yi domin shawo kan annobar cutar COVID-19.

A cikin wasikar, yarinyar ta bayyana cewa, "ni ba diyar masu kudi bace. Ina da asusun tara kudi, inda na tara jimillar N2350 da nake son sadaukar da su ga gidan marayu na garin Warri, jihar Delta. Amma, yanzu na fahimci cewa gwamnati ta fi bukatar tallafin kudin. Kudin babu yawa, amma ka daure ka karba saboda ni yarinya ce."

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Vera daliba ce da dokar rufe makarantu ta tilasta wa zama a gida.

"Rufe makarantu saboda annobar cutar coronavirus ya kawo tsaiko a harkar karatunmu, amma hakan shine mafi alheri," a cewar karamar yarinyar.

Ko a jiya, Talata, Legit.ng ta wallafa rahoton cewa shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin kasashen ketare, Yussuf Buba, dan jam'iyyar APC, ya kafa wata gidauniya tare da sadaukar da dukkan albashinsa na kowanne wata ga jama'arsa domin rage musu radadin matsin da annobar cutar covid-19 ta haifar.

DUBA WANNAN: Ba zata sabu ba: IPMAN ta mayar wa da FG martani a kan sake rage farashin litar man fetur

A wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Abuja, Buba ya bayyana cewa gidauniyarsa, wacce ya sakawa suna 'Yusuf Captain Buba coronavirus Trust Fund', za ta samar da kayan kare kai daga kamuwa da kwayar cutar coronavirus ga jama'ar mazabarsa da ke jihar Adamawa.

Dan majalisar, mai wakiltar mazabar Gombi da Honng, ya ce akwai bukatar kyakyawan shiri tare da samar da sahihan bayanai ga jama'a domin yakar kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng