Najeriya ta na cikin karancin na’ura a tsakiyar annobar COVID-19

Najeriya ta na cikin karancin na’ura a tsakiyar annobar COVID-19

A daidai lokacin da cutar COVID-19 ta ke cigaba da ratsa jihohin Najeriya, bincike ya nuna cewa ana fama da karancin na’urar numfashi a wasu jihohi.

Daily Trust ta fitar da wani dogon rahoto a Ranar Laraba game da yadda na’urar taimakawa numfashi wanda ake kira ‘Ventilators’ su ka yi kadan.

A cikin jihohin Najeriya 16, akwai na’urar Ventilator 169 ne kacal. Abin da hakan ke nufi shi ne kusan na’ura goma ake da su a kowace jiha a Najeriya.

Hakikanin alkaluman da ke kasa sun nuna cewa wasu Jihohi su na fama ne da wannan na’ura wanda ta ke taimakawa masu cutar COVID-19 guda biyar.

A wasu jihohin ma babu wannan na’ura ko guda. Gwamnatocin jihohi su na ikirarin sun bada kudi domin sayen wadannan kayan aiki amma ba su iso ba.

Jihohin da wannan bincike da Daily Trust ya shafa su ne: Kano, Ogun, Edo, Delta, Adamawa, Kwara, Bayelsa, Katsina, Borno, Yobe, Benue, da jihar Bauchi.

KU KARANYA: Coronavirus: Najeriya za ta kara sallamar wadanda su ka warke

Najeriya ta na cikin karancin na’ura a tsakiyar annobar COVID-19
Shugaban hukumar NCDC mai takaita yaduwar cuta Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Sauran ragowar jihohin su ne: Kaduna, Ebonyi, Gombe da kuma jihar Filato. Kudin kowane na’urar mai taimakawa numfashi bai wuce Miliyan 9 zuwa Miliyan 18.

Binciken bai iya gano adadin na’uran da ke Abuja da Legas ba inda wannan cuta ta fi kamari. Amma a jihar Kano akwai wadannan na’urar akalla 27 a asibitoci.

A jihar Edo, gwamnatin jihar ta ce ta na da na’urar ‘Ventilators’ 25. A Benuwai ma akwai 19. Na’urori 5 ake da su a asibitocin jihohin Bayelsa da jihar Adamawa.

A jihar Katsina da Benuwai da Bauchi akwai na’urori 5, 6, 4 kamar yadda rahoton ya bayyana. Na’urori 8 da ake da su a Filato, a jihar Borno kuma akwai akalla 15.

A kaf asibitocin Nasarawa da jihar Kebbi babu wannan na’urar ko da guda. Kusan dai haka wannan lamari ya ke asibitocin da ke jihar Gombe a Arewa maso Gabas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng