Ba zata sabu ba: IPMAN ta mayar wa da FG martani a kan sake rage farashin litar man fetur

Ba zata sabu ba: IPMAN ta mayar wa da FG martani a kan sake rage farashin litar man fetur

Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu (IPMAN) reshen jihar Kano ta ce mambobinta ba zasu iya sayar da litar man fetur a kan sabon farashin N123.50 ba kamar yadda gwamnatin tarayya ta rage.

A saboda haka, kungiyar ta yi kira ga dukkan mambobinta a kan su sayar da litar man fetur a kan farashin N125 har zuwa lokacin da man da suke da shi zai kare.

Shugaban kungiyar IPMAN a jihar Kano, Alhaji Bashir Danmalam, ne ya bayar da wannan umarni yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano.

A cewarsa, mambobin kungiyarsu ba zasu yi biyayya ga umarnin sabon farashin litar man fetur ba sai sun sayar da dukkan man fetur da suke da shi yanzu.

Ba zata sabu ba: IPMAN ta mayar wa da FG martani a kan sake rage farashin litar man fetur

IPMAN ta mayar wa da FG martani a kan sake rage farashin litar man fetur
Source: UGC

A jiya, Talata, ne gwamnati tarayya ta sanar da sake farashin litar man fetur zuwa N123.50 kowacce lita daya.

DUBA WANNAN: Dokar rufe kasuwanni bata shafi shagunan gefen titi da cikin unguwanni ba - Rundunar 'yan sanda

A wani jawabi da hukumar kula da farashin man fetur (PPPRA) ta fitar da yamacin ranar Talata, sakataren hukumar, Mista Abdulkadir Saidu, ya ce rsabon farashin litar man zai fara aiki ne daga ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2020.

A cewar jawabin, "bisa dogaro da sabon tsarin duba farashin man fetur a gidajen mai kowanne wata, mu na sanar da rage farashin litar man fetur zuwa N123.50."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel