Hadimin Shugaban kasa, Ahmaad ya karyata jita-jitar sallamar Kyari

Hadimin Shugaban kasa, Ahmaad ya karyata jita-jitar sallamar Kyari

A cikin makon nan ne wani labarin karya ya rika yawo na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori babban Hadiminsa Malam Abba Kyari daga aiki.

Abba Kyari wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya ya na fama da cutar Coronavirus, wanda ta sa shi dole ya shiga jinya a halin yanzu.

Daya daga cikin Hadiman shugaban kasa, Bashir Ahmaad ya yi magana game da wannan jita-jita da ake yi, inda ya shaidawa jama’a cewa babu gaskiya a labarin.

Malam Bashir Ahmaad ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari bai maye gurbin Abba Kyari da Abiola Ajimobi ba, duk da labarin ya karada dandalin WhatsApp.

“Kuma dai wani labarin bogi ya fara yawo a zaurukan dandalin WhatsApp cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari (@MBuhari) ya tsige Mallam Abba Kyari.”

KU KARANTA: Kyari ya bayyana halin da ya ke ciki bayan kamuwa da COVID-19

Bashir Ahmaad a shafinsa na Tuwita, ya cigaba da cewa: “Sannan Buhari) ya maye gurbinsa da tsohon gwamna Abiola Ajimobi, Ku yi watsi da wannan labari.”

Ahmad ya ce sam ka da jama’a su dauki wannan labari domin babu gaskiya a cikinsa gaba daya. Ajimobi tsohon gwamnan jihar Oyo ne wanda ya sauka a 2019.

Malam Ahmaad ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Tuwita a Ranar 31 ga Watan Maris, 2020. Ahmaad ya yi wannan jawabi na karin haske ne cikin tsakar dare.

Haka zalika Mai taimakawa shugaban kasar wajen harkokin sadarwa ta kafafen zamani, ya ce labarin da ke yawo na cewa za a rabawa jama’a kudi ba gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel