Dokar rufe kasuwanni bata shafi shagunan gefen titi da cikin unguwanni ba - Rundunar 'yan sanda

Dokar rufe kasuwanni bata shafi shagunan gefen titi da cikin unguwanni ba - Rundunar 'yan sanda

Shagunan saye da sayarwa da ke cikin unguwanni da gefen hanya za su iya cigaba da harkokinsu na kasuwanci matukar sun girmama dokar nesanta da taron jama'a da suka wuce 20, kamar yadda rundunar 'yan sandan jihar Legas ta bayyana ranar Lahadi.

Rundunar 'yan sandan ta bayyana hakan ne a matsayin martani a kan rahoton da ta samu a kan cewa masu kananan shaguna da ba a cikin kasuwa suke ba sun fara daina bude shagunansu domin yin biyayya ga dokar rufe kasuwanni da walwalar jama'a.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya bayyana cewa dokar bata shafi masu irin wannan shaguna ba, koda kuwa ba kayan abinci da magunguna suke sayarwa ba.

Da yake bayar da misali, Elkana ya ce mai shagon aski ko wanke kai zasu iya bude shagunansu domin yin sana'arsu matukar ba zasu tara jama'ar da suka wuce 25 a lokaci daya ba, kuma zasu kiyaye dokar nesanta.

Dokar rufe kasuwanni bata shafi shagunan gefen titi da cikin unguwanni ba - Rundunar 'yan sanda
Dokar rufe kasuwanni bata shafi shagunan gefen titi da cikin unguwanni ba - Rundunar 'yan sanda
Asali: Original

Elkana ya kara da cewa rundunar 'yan sanda ta bukaci jami'anta su nuna tausayi da jin kai yayin da suke aikin tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga dokar killace kansu a cikin gidajensu, kamar yadda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni yayin jawabin da ya gabatar ga 'yan kasa a daren ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta sake rage farashin litar man fetur a karo na biyu

A wani labarin mai nasaba da wannan, rundunar 'yan sanda a jihar Filato ta kira shugaban majalisar koli ta malaman darikar Izalatil Bid'a Wa'ikamatis Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, tare da yi masa tambayoyi an kan rashin biyayya ga umarnin jiha na hana dukkan wani taro har na addini a jihar saboda gujewa kamuwa da kwayar coronavirus.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya shaidawa manema labarai, da yammacin ranar Talata, cewa sun gayyaci Sheikh Jingir zuwa hedikwatar saboda ya jagoranci magoya bayansa sallar Juma'a duk da an saka dokar hana taron jama'a.

A cewar ASP Gabriel, kwamishinan 'yan sandan jihar, Isaac Akinmoyed, ya shaidawa Sheikh Jingir cewa rundunar 'yan sanda ba zata lamunci irin wannan halin ba a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng