Hotuna: Yadda aka binne wani mutumi da ya mutu a cikin motar da yafi kauna a duniya
- Jama'a mazauna wani kauye da ke gabashin Cape a kasar Afrika ta Kudu sun sha matukar mamaki da al'ajabi
- An birne wani tsoho mai shekaru 74 a cikin motar shi kirar kamfanin marsandi don cika mishi burin shi da wasiyyarshi
- Kamar yadda iyalanshi da dangi suka sanar, tsohon masoyin motocin kamfanin marsandi ne kuma da kanshi ya siya wannan motar tare da bada wasiyyar a birne shi a ciki
A maimakon akwatin gawa, wani mutum da ya mutu a gabashin Cape da ke kasar Afrika ta Kudu an birne shi a motar shi.
A takaice dai, a shekaru biyu da suka gabata ne Tshekedi Pitso ya ba iyalan shi mamaki lokacin da ya sanar dasu cewa yana so a birneshi a cikin motar da yafi so.

Asali: Facebook
Pitso mai shekaru 72 a wancan lokacin ya siya motar kirar marsandi E500 inda ya hada ta da sauran motocin alfarmar da ya mallaka, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
Diyar yayan Pitso, Sefora mai shekaru 49 ta ce da farko dai iyalan shi sun matukar shan mamakin labarin. Sau da yawa yana tsara yadda yake so a birneshi.
KU KARANTA: Mai cutar Coronavirus da aka killace ana yi mata magani ta gudu daga asibiti
Kauyen Jozanashoek da ke Sterkspruit a gabashin Cape, inda Pitso yake shugaban kuma dan jam'iyyar UDM, sun matukar firgita bayan da aka birne shugaban a mota kira Marsandi.
"Kawu na ya bayyana cewa yana so a birne shi a cikin motar shi. Masoyin motocin kamfanin marsandi ne. A matsayinmu na dangi da iyalai, dole ne mu cika mishi burin shi," tace.
Mazauna kauyen kuwa sun sha kallo cike da mamakin yadda aka haka kabarin shi mai matukar fadi wanda ya dauki motar.
An saka mishi kaya launin farare sannan an sanya mishi damarar mai tuki tare da sargafo hannayenshi a kan sikiyarin motar.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng