Mai cutar Coronavirus da aka killace ana yi mata magani ta gudu daga asibiti

Mai cutar Coronavirus da aka killace ana yi mata magani ta gudu daga asibiti

- Rahotanni sun bayyana cewa wata mara lafiya dauke da cutar coronavirus ta gudu daga asibiti a kasar Ghana

- Kamar yadda aka bayyana, matar wacce ke da shekaru 20 da doriya ta tsallake katangar cibiyar killacewar inda ta shiga gari abinta

- Ministan Arewacin kasar, Saeed ya tabbatar da cewa abun fargaba ne da alhini amma za su shawo kan matsalar da gaggawa

An gano cewa wata marar lafiya mai dauke da cutar covid-19 ta tsere daga inda aka killace ta a kasar Ghana.

Kamar yadda jaridar Ghana City News ta bayyana, mara lafiyan na daya daga cikin mutane takwas 'yan asalin kasar da kwanan nan aka gano suna dauke da muguwar cutar a Ghana.

Ministan yankin Arewa, Salifu Saeed ya tabbatar da cewa mara lafiyar wacce ta kasance mace mai shekaru 20 da doriya, ta tsallake katanga ne tare da barin kayanta a cibiyar killacewar da ke Tamale a ranar Litinin.

Ya kwatanta lamarin da abun tsoro da fargaba don kuwa tana dauke da muguwar cutar.

KU KARANTA: Mutum shida sun mutu daya rai a hannun Allah bayan babbar motar Dangote ta bi ta kansu

"Tun jiya, har zuwa safiyar yau banyi bacci ba tare da jami'an tsaro na. Na bada umarnin cewa su yi amfani da duk wata hanyar da ta dace don kamota," Saeed yace.

Tun farko dai an gano cewa 'yan sanda biyu da sojoji biyu ne ke gadin cibiyar killacewar inda ake kula da masu cutar.

Saeed ya yi kira ga 'yan kasar da su kwantar da hankalinsu don za a shawo kan lamarin.

"Jama'armu su kwantar da hankulansu don muna matukar kokari don tabbatar da cewa hankula basu tashi ba. Kada wanda ya firgita don daga ni har jami'an tsaro na muna kokari."

Amma kuma, wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce an kama mara lafiyar a Kumbungu amma ba a sanar da jami'an tsaro ba.

A ranar 31 ga watan Maris din 2020, Ghana na da masu cutar coronavirus 152.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng