Coronavirus: Mu na neman kusan mutane 5000 inji Shugaban hukumar NCDC

Coronavirus: Mu na neman kusan mutane 5000 inji Shugaban hukumar NCDC

A yunkurin da ake yi na shawo kan annobar COVID-19 a Najeriya, hukumar NCDC ta bayyana cewa ta na bibiyar mutanen da ake zargin sun kamu da wannan cutar.

NCDC mai takaita yaduwar cuta a Najeriya ta bayyana wannan ta bakin Darektanta, Dr. Chikwe Ihekweazu, sa’ilin da ya zanta da ‘Yan Jarida a birinin tarayya Abuja.

A Ranar Talatar nan ne kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar COVID-19 a Najeriya, ta sake yin wani zama na musaman da ‘Yan jarida a Abuja.

Chikwe Ihekweazu ya ce har yanzu dabarun takaita wannan cuta NCDC ta ke amfani da shi. Ihekweazu ya ce NCDC na da damar bankado duk masu dauke da cutar.

Shugaban hukumar ta NCDC ya shaidawa ‘Yan jaridar cewa lalubo wadanda su ka yi mu’amala da masu wannan cuta abu ne mai wahala da kuma matukar cin lokaci.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Za a sallami wadanda su ka warke daga Coronavirus

Dr. Ihekweazu ya ce akwai mutane kimanin 5, 000 a fadin jihohin Najeriya da su ka yi mu’amala da wadanda su ke dauke da kwayar cutar COVID-19 mai hana numfashi.

Babban Likitan ya nuna cewa akwai bukatar jama’a su guji haduwa a daidai wannan lokaci domin ta haka ne kawai za a rage yaduwar wannan cuta da ta zama annoba.

Wadanda yanzu ake zargin sun kamu da wannan cuta sun hada da wadanda ke fama da wahalar numfashi ko larurar mura da tari a cikin kwanaki goma da su ka wuce inji sa.

Shi ma Ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya tofa albarkacin bakinsa, inda ya bayyana kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi game da sha’anin yin gwajin cutar ta COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel