Gwamnan jahar Imo ya yi awon gaba da babban akanta, ya nada sabo nan take

Gwamnan jahar Imo ya yi awon gaba da babban akanta, ya nada sabo nan take

Sabon gwamnan jahar Imo, Sanata Hope Uzodinma ya sanar da tsige babban akanta na jahar, Donald Igbo daga mukaminsa, sa’annan ya nada Mista Obieze Chukwukama a matsayin sabon babban akantan jahar.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Oguwike Nwachukwu wanda ya bayyana cewa nadin Mista Obieze ya fara aiki ne nan take. “Gwamna Hope Uzodinma ya nada Obieze Valentine Chukwukama a matsayin sabon babban akanta.” Inji shi.

KU KARANTA: Annobar Corona: Gwamnatin Saudiyya ta umarci Musulmai su dakatar da batun aikin Hajji

Wasikar ta kara da cewa: “Don haka muna kira da ku dakatar da duk wani cinikayya da tsohon babban akantan, Donald Igbo, kuma ka gudanar da dukkanin sauye sauyen da suka kamata game da asusun jahar Imo.”

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Imo Hope Uzodinma ya nada Alhaji Ibrahim Sulaiman a matsayin hadiminsa mai bashi shawara a kan harkokin al’ummar yankin Arewa da kuma kungiyar Miyetti Allah mazauna jahar.

Ko a ranar Litinin, 30 ga watan Maris sai da Alhaji Ibrahim tare da Sarkin Hausawan jahar Imo, Alhaji Auwalu Baba Suleiman suka fita zuwa unguwannin Hausawa domin wayar da kawunansu game da illar annobar nan ta Coronavirus.

A wani labari kuma, karamin ministan kiwon lafiya, Dakta Olurunnimbe Mamore ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na kashe kimanin naira dubu 10 wajen gudanar da gwajin Coronavirus ta hanyar amfani da tsarin hukumar kiwon lafiya ta Duniya, WHO, dake bayar da gamsashshen sakamako.

Mamora ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake ganawa da yan jaridu a babban birnin tarayya Abuja, inda yace amma gwamnati ba wai ta damu da kashe kudin bane, tunda dai ana samun sahihin sakamako.

A hannu guda, gwamnatin kasar Saudiyya ta nemi musulman duniya da su dakatar da batun zuwa aikin Hajjin bana har sai yadda hali yayi game da annobar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, watau Coronavirus.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta bayyana cewa kasar Saudiyya ta dakatar da aikin Umrah tun a farkon shekarar nan sakamakon tsoron da take ji na shigar mata da cutar Coronavirus cikin kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel